Shekau ya na neman Allah ya kare shi daga sojojin Najeriya

Shekau ya na neman Allah ya kare shi daga sojojin Najeriya

A cikin wani sabon sako na daukan sauti, an ji muryar jagoran kungiyar ta'adda ta Boko Haram, Abubakar Shekau, yana rusa kuka yana neman kariyar Allah daga sojojin Najeriya.

A baya bayan nan, babu sassauci rundunar sojojin Najeriya ta kara kaimi wajen kai hare-hare, tare da samun jerin nasarori a kan 'yan Boko Haram musamman a yankunan da ke gabar tafkin Chadi.

Cikin sakon daukan sauti na tsawon minti daya da dakiku 22 da jaridar Daily Nigerian ta saurara, an ji muryar Shekau cikin harshen Kanuri yana neman kariyar Allah daga wutar da sojojin Najeriya suka kunno masa.

Shekau ya misalta matsin lambar da sojojin Najeriya suka yi masa a matsayin 'aikin shaidan', lamarin da ya ce shi da mabiyansa suna cikin mawuyacin hali a wannan wata mai Albarka na Ramadana.

"In dai zaluncin sojojin Najeriya ne, to Ya Allah ka tsare mu daga sharrrinsu. Ya Allah ka tabbatar da mu a kan addininka. Ya Allah babu abin da muka sani kuma babu abin da zamu iya isarwa kawunanmu. Kai ne mai jibintar lamarin Ya Ubanginjinmu."

"Mun kaurace wa Izala saboda mu yi addininka na gaskiya; mun bar Tijjaniya saboda mu daidaita a kan tafarkin ka na gaskiya; mun barranta daga Shi'a domin yin addininka na gaskiya; mun bar iyayenmu da 'yan uwanmu domin mu tsira da addininka na gaskiya."

Saboda addininka muke yanka wuyan bayinka da wuka; amma a yau suna kokarin sauya mu zuwa wani addini sabanin naka. Ya Ubangiji kayi mana rahama domin falalar watan Ramadan; Ya Allah ka kawo mana sauki a cikin wannan wata mai Albarka.

"Ya Allah ka bamu nasara a kan makiyanmu. Ya ku yan'uwa don Allah, ku yiwa Allah biyayya ku taimaka min da addu'o'i ta neman kariyarsa."

"Ya Allah ka mu ikon riko da Alkur'ani. Allah kai ne mafi sani. Tsira da aminci su tabbata a kan Annabin ka, kuma dukkanin godiya ta tabbata a gare ka," Shekau ya ci gaba da shessheka.

Shekau da Bukarti

Shekau da Bukarti
Source: Facebook

Wani lauya mai kare hakkin dan Adam kuma manazarcin rikici wanda ya karanci kungiyar Boko Haram sama da shekaru goma, Bulama Bukarti, ya yi magana a kan sakon muryar.

A cewar Bulama, "wannan shi ne karo na farko da muka fara jin Shekau yana irin wannan kuka, wanda ya nuna cewa wani mummuna abu na faruwa da shi da kuma mabiyansa."

KARANTA KUMA: WHO ta lissafa abubuwa 6 Buhari da sauran shuwagabanni za su yi kafin su cire dokar kulle gaba daya

"Shekau din da muka sani tsagera ne kuma marar tausayi mai yawan izgilanci da nuna iko. Wannan abu da muka ji bakon abu ne wanda ya nuna cewa kungiyarsa na fuskantar matsin lamba mai barazana ga kasancewarta a doron kasa."

"Duk abin da zai sa Shekau ya zubar da hawaye irin haka ba karami bane. Kuma ina ganin babbar barazanar kawo karshen kungiyar ita ce ta janyo haka biyo bayan matsin lambar da sojojin Najeriya ke yi musu."

"A 'yan kwanakin nan rundunar sojin kasan Najeriya na ci gaba da sakin rahotanni da hotunan nasarorin da ta ke samu, haka kuma ita kanta kungiyar Boko Haram tana bayyana irin raunin da ta ke fuskanta. Wannan shi ne dalilin da ya sa Shekau ya zubar da hawaye domin kuwa yana tunanin karshensa ya zo," inji Bulama

Sai dai Bulama ya bayyana cewa, wannan sakon murya ba ya nuna cewa jagoran na Boko Haram ya fara saduda kuma ba ya nufin yana neman sasanci.

"Amma kada a yi kuskuren fahimta, domin kuwa Shekau ba zai taba ja da baya ba kuma ba zai mika wuya ba. Yana nan a kan bakansa kuma ya gwammace ya mutu kamar yadda sakon sautin muryar ta sa ya nuna."

"Kuma tarihi ya nuna mana cewa, Boko Haram na da ikon tashin hankalin kasar nan a kowane lokaci duk da irin nasarorin da aka samu a kanta a yanzu."

"Da wannan ne nake shawartar rundunar sojin kasan Najeriya ta kara kaimi gami da zage dantsenta wajen yi wa 'yan ta'addan luguden wuta, wannan ba lokacin da za a huta bane, lokaci ne da za a kara jajircewa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel