Coronavirus: Za mu bi diddigin yadda Buhari zai kashe bashin N1.3trn - Majalisa

Coronavirus: Za mu bi diddigin yadda Buhari zai kashe bashin N1.3trn - Majalisa

Kakaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa majalisa za ta bi diddigin yadda gwamnatin Buhari za ta kashe bashin da bankin lamuni, IMF ta baiwa Najeriya.

Femi ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da kungiyoyi masu zaman kansu, inda yace da haka ne zasu tabbata an kashe kudaden bisa tsarin da aka amso su.

KU KARANTA: Abubuwa 13 game da Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya

A watan Afrilu ne IMF ta amince da bukatar Najeriya na neman taimakon kudin gaggawa da suka dala biliyan 3.4 domin cike gibin da ta samu a kudadenta a dalilin barkewar COVID-19.

Daily Nigerian ta ruwaito kakaakin yace akwai kudurin dokar farfado da tattalin arziki da majalisar take aiki a kansa a yanzu, kuma da zarar ta gama zata gabatar da shi don tattaunawa.

Dokar za ta rage haraji da kashi 50 ga kamfanonin da basu sallami ma’aikatansu saboda Corona ba, duk wani batu da ya shafi yaki da COVID-19 za su dauke shi da matukar muhimmanci.

Coronavirus: Za mu bi diddigin yadda Buhari zai kashe bashin N1.3trn - Majalisa
Buhari, Lawan, Gbajabiamila Hoto: NASS
Asali: UGC

“A yanzu haka kudurin dokar na gaban majalisar dattawa, kuma za mu cigaba da tuntubarsu don ganin ya zama doka, haka akwai wani sabon kuduri na biyu dake majalisar wakilai, zai fi na farkon amfani ma saboda muna duba hanyar da ta fi dacewa don shawo kan COVID-19 ne.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sanar da kwace dala dubu 300 daga hannun wani mutumi dan kasar China, Li Yan Pin.

Hukumar EFCC ta bayyana Alkalin babbar kotun tarayya, Mai Sharia Babatunde Quadri ne ya bayar da izin kwace makudan da suka kai kimanin naira 116, 853, 003.71.

Sanarwa daga hukumar EFCC da ta samu sa hannun kakaakinta, Dele Oyewale ta bayyana cewa Alkalin ya fasa daure mutumin saboda yana dauke da alamomin cutar Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng