Kowa ya raina gajere ya taka kunama: El-Rufai ya fadi sunan jagoran tafiyarsu ta ‘Kungiyar gajerun Najeriya’

Kowa ya raina gajere ya taka kunama: El-Rufai ya fadi sunan jagoran tafiyarsu ta ‘Kungiyar gajerun Najeriya’

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban tafiyarsu ta kungiyar gajerun Najeriya.

Gwamnan, wanda shi ma ‘Baba karami’ ne ya bayyana haka ne a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Twitter, a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun shekarar 2020.

KU KARANTA: Abubuwa 13 game da Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya

A cewar Gwamna El-Rufai, mataimakin shugaban kasa Osinbajo wakilinsu a matakin kololuwa na shugabanci a Najeriya, don haka su ma ba’a barsu a baya a sha’anin mulki ba.

El-rufai ya bayyana haka ne cikin raha yayin da yake tsokaci ga wani bidiyon hira da ya taba yi da wani mai shirin barkwanci Teju Babyface a shekarar 2010 a jahar Legas.

A cikin wannan tsohon hira da yayi a shekarar 2010, El-Rufai ya bayyana ma Teju cewa a da shi ne babban sakataren kungiyar gajerun mutanen Najeriya, wanda hakan ya baiwa kowa dariya.

Ya cigaba da bayyana yadda yayi ta kokarin samun soyayyar kyawawan yan mata a zamanin da yake matashi, amma matsalar sun fi shi tsawo,.

Har sai lokacin da Allah Ya hada shi da matarsa, wanda ya fi ta tsawo da inci 1.

“Eh…Na tuna wannan a hirar da na yi da Tejubabyfacetv a shekarar 2010, kalli yadda lokaci ke gudu. Mai girma mataimakin shugaban kasa Osinbajo ne shugaban gajerun mutanen Najeriya a yanzu, don haka muna da wakilci a matakin farko na shugabanci. Nagode Teju.” Inji shi.

Wannan tsokaci na gwamnan ya janyo martani da dama, dayawa daga ciki sun yaba da rahar da gwamnan yayi.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya janye jikinsa daga siyasa tun bayan faduwarsa zabe a shekarar 2015 ne don ya kula da gidauniyarsa.

Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu yayin da gwamnan jahar Bayelsa, Duoye Diri ya rantsar da shuwagabannin jam’iyyar PDP a garin Bayelsa.

Jonathan yace yana janye jikinsa daga siyasa, amma kuma ya fahimci jama’a da dama basu fahimce shi ba, saboda basu gane muhimmancin matakin daya dauka a wajen sa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel