Dan kasar China mai cutar Coronavirus ya yi asarar $300,000 a hannun EFCC

Dan kasar China mai cutar Coronavirus ya yi asarar $300,000 a hannun EFCC

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sanar da kwace dala dubu 300 daga hannun wani mutumi dan kasar China, Li Yan Pin.

EFCC ta bayyana a shafinta na Facebook Alkalin babbar kotun tarayya, Mai Sharia Babatunde Quadri ne ya bayar da izinin kwace makudan da suka kai kimanin naira 116, 853, 003.71.

KU KARANTA: Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2

Sanarwa daga hukumar EFCC da ta samu sa hannun kakaakinta, Dele Oyewale ta bayyana cewa Alkalin ya fasa daure mutumin saboda yana dauke da alamomin cutar Coronavirus.

“Alkalin ya baiwa EFCC daman rike kudin a hannunta na dindindin biyo bayan bukatar hakan da EFCC ta mika ma kotun. An tuhumi Yan Pin da laifin boye wasu kudi ne bayan an kama shi a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe dake Abuja.

“Yan Pin bai bayyana gaskiyar kudaden dake tare da shi ba yayin da yayi kokarin ficewa daga Najeriya zuwa China.

"Alkalin yace masu kara sun gamsar da kotu da hujjojinsu, don haka ya kama wanda ake kara da laifi kamar yadda sashi na 2 na sashi na 5 na dokokin laifin kudi na shekarar 2011 suka tanada.

“Sai dai lauyan wanda ake kara ya nemi sassauci daga wajen kotu saboda a cewarsa wanda yake karewa ya zuba makudan kudade a Najeriya don cigaban kasar, kuma duba da cewa ba shi da lafiya, haka zalika ba’a taba kama shi da laifi ba.” Inji shi.

Daga nan sai Alkalin ya bada umarnin kwace kudin, sa’annan ya rangwanta masa zaman gidan yari sakamakon cutar Coronavirus da yake fama da ita.

A hannu guda, Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da samun mutum na farko daya mutu a sakamakon mugunyar cutar nan ta Coronavirus mai sarke numfashin dan Adam a jahar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jahar, Idris Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi game da aikin kwamitinsu.

Idris ya bayyana mamacin a matsayin dan shekara 50, wanda yace cutar ciwon siga na damunsa, kuma ya rasu ne da misalin karfe 4 na rana a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel