Biyafara: Jagoran IPOB Nnamdi Kanu ya sabunta rikicinsa da Uwazuruike

Biyafara: Jagoran IPOB Nnamdi Kanu ya sabunta rikicinsa da Uwazuruike

Shugaban kungiyar nan ta IPOB mai fafutukar Biyafara, Mazi Nnamdi Kanu, ya sabunta kullaliyar rigimarsa da takawaransa na kungiyar BIM, Mista Ralph Uwazuruike.

Jaridar Daily Sun ta ce Nnamdi Kanu ya fito ya na zargin jagoran na kungiyar BIM, Ralph Uwazuruike da yin watsi da ainihin gwargwarmyayar da kungiyoyinsu ta ke kai.

Nnamdi Kanu ya yi jawabi ne a gidan rediyon Biyafara, ya na tir da Ralph Uwazuruike a kan daukar batun da ya shafi mutanen Ibo da ya yi, ya kai gaban zauren hukumar UNPO.

Kanu ya ke cewa zuwa gaban UNPO da ke birnin Hague a kasar Netherlands ya ragewa Ibo matsayi. Jagoran na IPOB ya ce bai kamata waninsu ya rika kula irinsu UNPO ba.

A cewar Nnamdi Kanu, manyan kungiyoyin da ake ji da su a yau kamar kungiyar kasasshen Afrika ta AU da majalisar dinkin Duniya watau UN sun san da zaman Biyafaran.

KU KARANTA: Mutanen Ibo ba su bukatar mulkin Najeriya - Nnmadi Kanu

Biyafara: Jagoran IPOB Nnmadi Kanu ya sabunta rikicinsa da Uwazuruike
Nnamdi Kanu ya soki zuwa gaban UNOP da Ralph Uwazuruike ya yi
Asali: Facebook

A dalilin haka ne shugaban kungiyar IPOB ya ke ganin tunkarar kungiyar UNOP da Ralph Uwazuruike ya yi, kokarin maida tafiyar sauran masu fafatukar Biyafara baya ne.

“Saboda kawai ya samu gindin zama, ganin ya san cewa kwanan nan za a samu kasar Biyafara, sai ya ruga gaban UNPO wanda matsayinta daya da kungiyarmu ta majalisar Ibo.”

Nnamdi Kanu ya cigaba da cewa: “Babu abin da ya hada hukumar UNPO da Biyafara, (Ralph) Uwazuruike ya batawa Biyafara suna, mutumin da ya gina gidansa da kudin Biyafara.”

“Ya kai Biyafara yanzu gaban UNPO, UNPO ta na cikin UN ne? kungiyar da ba ta da hadi da Biyafara. Ba za ka iya gina Biyafara a kan karya ba, mu na ja maka kunne.” Inji sa.

“Jinin Najeriya ne a jikinka, ka daina yaudarar kanka da jama’a. Kwanan nan za mu samu ‘yanci ba da gumin ka ba. Zan zo Amurka in yi magana, za a tarbe ni, za a ga goyon baya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel