Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2

Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska dake rufe hanci da baki domin dakile yaduwar mugunyar cutar nan mai sarke numfashi, watau COVID-19.

Hadimin Ganduje a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a ranar Litinin, 11 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu

Takunkumin wanda aka samar da su guda miliyan 2 tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jahar, za’a rabar da su ne a kananan hukumomin jahar guda 44.

“Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da rabon safar baki da hanci wato face mask guda 2 Million wanda zaa raba a fadin jihar Kano baki daya.

“Gwamnatin jiha ce ta samar da guda 1Million sai kuma gamaiyar kananen hukumomi na jihar Kano 44 su kuma suka samar da guda 1Million.” Inji shi.

Idan za’a tuna, gwamnatin jahar Kano ta bayyana sanya takunkumin fuska wajibi ga duk wani mazaunin jahar Kano domin a samu daman shawo kan wannan annoba.

A hannu guda kuma, kungiyar Telolin jahar Kano ta dukufa haikan don bayar da nata gudunmuwa a yakin da ake yi da cutar Coronavirus.

Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2

Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2 Hoto: Salihu Yakasai
Source: Facebook

Yakasai yace kungiyar ta kuduri bayar da tallafin takunkumin da a yanzu haka take dinkawa, kuma nan bada jimawa za ta kammala aikin dinkasu domin a raba ma jama’a.

Haka zalika gwamnan na Kano Ganduje ya ce gwamnatinsa ta dauki mutanen da ta kira 'dakarun tsafta' wadanda za su yi yaki da cutar korona.

"Daukarku wannan aiki da aka yi, an yi tunanin kwarai da gaske; aka zabo matasa, maza da mata, masu jini a jiki wadanda za su shiga lungu-lungu da kasuwanni a tabbata cewa an yi tsafta yadda ya kamata" in ji Gwamna Ganduje.

A yanzu jahar Kano na da mutane 666 da suka kamu da cutar Coronavirus, mutane 63 sun mutu yayin da 32 suka rigamu gidan gaskiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel