Rigar kowa: Ibrahim Inuwa, shugaban NSE na farko daga arewa, ya mutu

Rigar kowa: Ibrahim Inuwa, shugaban NSE na farko daga arewa, ya mutu

Tsohon shugaban kungiyar injiniyoyin Najeria (NSE), Injiniya Ibrahim Khaleel Inuwa, ya mutu, kamar yadda Legit.ng ta samu labari.

Marigayi Inuwa ya kasance shugaban kungiyar NSE na 16 sannan mutum na farko daga yankin arewacin Najeriya da ya shugabantar kungiyar NSE.

Ya mutu a yau, Litinin, a gidansa da ke birnin Kano.

Shugaban kungiyar NSE mai ci, Injiniya Babagana Mohammed, ya tabbatar da mutuwar marigayi injiniya Inuwa.

Marigayin ya taba rike mukamin kwamishinan raya karkara da kuma kwamishinan lafiyar dabbobi da gandun daji na jihar Kano.

Rigar kowa: Ibrahim Inuwa, shugaban NSE na farko daga arewa, ya mutu
Marigayi Ibrahim Khaleel Inuwa
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na 'facebook', Mohammed ya ce, "cikin juyayi da sallamawa ikon Allah, ina mai bakin cikin sanar da mutuwar daya daga cikin tsofin hazikan shugabanninmu, Injiniya Ibrahim Khaleel Inuwa, (shugaban NSE, 1989 - 1990).

DUBA WANNAN: Dokar kulle: Alkalan kotun tafi da gidanka sun sha da kyar a hannun fusatattun matasa a jihar Taraba

"Injiniya Inuwa ya mutu yau, Litinin, cikin salama a gidansa da ke rukunin gidajen NNDC a unguwar Sharada da ke birnin Kano.

"Ina mai mika sakon ta'ziyya ga iyalai da dangin mamacin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel