An kashe 'yan Najeriya 11 a cikin sati uku yayin tabbatar da dokar kulle - NHRC
- Hukumar kare hakin bil'adama ta kasa (NHRC) ta ce jami'an tsaro sun kashe mutane 11 bayan tsawaita dokar hana zirga - zirga
- A rahoto na farko da ta fitar kafin wannan, NHRC ta ce jami'an tsaro sun kashe mutane 18 a cikin sati biyu da saka dokar zaman gida
- A cikin sabon rahoton, NHRC ta ce ta samu korafi 104 na take hakkin bil'adama a cikin sati uku na tsawaita dokar kulle a sassan Najeriya
A kalla mutane 11 aka kashe a sassan Najeriya a cikin sati uku da suka gabata yayin tabbatar da dokar kulle da aka tsawaita saboda dakile yaduwar annobar korona a kasa.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa (NHRC) ta fitar a ranar Litinin.
NHRC ta ce jihar Abia ce a gaba da adada mutane hudu da aka kashe yayin tabbatar da dokar kulle.
A cikin rahoto na farko da ta fitar bayan shafe sati biyu da saka dokar kulle, NHRC ta bayyana cewa jami'an tsaro a Najeriya sun kashe mutane 18 yayin aikin tabbatar da dokar zaman gida, adadin da hukumar ta ce ya zarce na wadanda annobar korona ta kashe.
A cikin sabon rahoton, NHRC ta ce ta samu korafi 104 na take hakkin bil'adama a cikin sati uku na tsawaita dokar kulle a sassan Najeriya.
DUBA WANNAN: Takunkumin fuska ya zama dole a Kano, za a gurfanar da masu kunnen kashi - Ganduje
Babban sakataren NHRC, Barista Tony Ojukwu, ya ce bayan jihar Abia da aka kashe mutane hudu, an kashe mutane biyu a jihar Delta, yayin da aka samu rahoton mutuwar mutum daya a kowacce daga cikin jihohin Neja, Jigawa, Lagos, Anambra da Ribas.
Ojukwu ya ce jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe mutane 7 daga cikin mutanen 11, yayin da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC da wata hukumar tsaro a jihar Abia suka kashe mutum dai - dai.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng