Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu

Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu

Akalla mutane biyar ne suka mutu sakamakon wata sabuwar rikici da ta barke tsakanin kabilun Fulani da Tibabe a jahar Nassarawa.

Daily Trust ta ruwaito baya ga kisan kai da aka yi, mutane da dama sun jikkata a rikicin daya barke a lardin Kadarko, cikin karamar hukumar Keana, a kan iyakar Nassarawa da Benuwe.

KU KARANTA: Annobar Corona: Shugaban kasa zai bude Masallatai amma da sharadi a kasar Liberia

Wani dan kabilar ya bayyana cewa rikicin ya faro ne bayan wani dan Fulani ya gamu da wata mata yar tibi a gona, inda ya mata dukan kawo wuka haka nan ba tare da wani laifi ba.

Ihun da matar ta yi na neman agaji ya sa wani dan tibi dake noma a gonarsa ya yi kokarin kai mata dauki, amma bafulatanin ya fi karfinsa, kuma ya sassare shi a kai da hannu.

Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu

Rikici Hoto: Sunnewsonline
Source: UGC

“Ganin haka yasa matasan kabilar Tibi suka harzuka, suka tafi daukan fansa inda suka afka ma wasu yan Fulani da suka yi gudun hijira daga gari Udei na jahar Benuwe.

"Su ma yan Fulani sai suka sake yin kwamba, suka kai hari a ranar Asabar, inda suka kashe mata biyu a wata gona da misalin karfe 9 na safe.” Inji shi.

Amma wani jami’in kungiyar Miyetti Allah da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa matasan kabilar Tibi sun kashe musu Fulani guda uku kwanaki uku da suka wuce a Yelwata.

Shugaban karamar hukumar Keana, Adamu Adi Giza ya tabbatar da hare haren tsakanin kabilun biyu, kuma ya bada tabbacin hukumar na yin duk mai yiwuwa don shawo kan lamarin.

“Na samu labarin an kashe Fulani guda biyu, haka zalika an kashe mata yan kabilar Tibi guda biyu, amma har yanzu ban samu cikkaken rahoton lamarin ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wata baturiya yar shekarar 60 daga kasar Amurka ta rasu a wani Otal dake Warri bayan ta kawo ma saurayinta ziyara a jahar Delta.

Mai karatu, ba’a yi kuskure ba idan aka ce wannan baturiya ta kira ma saurayinta ruwa, saboda a yanzu haka yana can ido ya raina fata a hannun rundunar Yansandan jahar Delta.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito matar ta mutu ne bayan ta wasu alamu dake nuna ta kamu da annobar cutar Coronavirus mai sarke numfashin mutum.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel