Coronavirus: Saudiyya ta ninka harajin VAT sau 3, ta dakatar da kudin ‘bulus’ da take biyan yan kasa

Coronavirus: Saudiyya ta ninka harajin VAT sau 3, ta dakatar da kudin ‘bulus’ da take biyan yan kasa

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da sabbin matakan ceto tattalin arzikinta wanda ya girgiza sakamakon bullar annobar Coronavirus a kasar.

Ministan kudi, Muhammad Al Jadaan ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace matakan sun zama wajibi domin samar da isassun kudi ga gwamnatin saboda karyewar darajar fetir.

KU KARANTA: Annobar Corona: Shugaban kasa zai bude Masallatai amma da sharadi a kasar Liberia

Matakan da ta dauka sun hada da ninka harajin VAT daga kashi 5 zuwa kashi 15, sa’annan ta dakatar da tsarin biyan kudin alawus ga yan kasa, kamar yadda ministan ya bayyana.

Coronavirus: Saudiyya ta ninka harajin VAT sau 3, ta dakatar da kudin ‘bulus’ da take biyan yan kasa
Sarki Salmanu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

“An yanke shawarar daina biyan alawus ga yan kasa daga watan Yuni na shekarar 2020, kuma harajin VAT za’a ninka shi daga kashi 5 zuwa kashi 15 daga 1 ga watan Yuli.” Inji Minista Jadaan.

Kamfanin watsa labaru na kasar Saudi ta ruwaito Ministan yana fadin wadannan matakai zasu tara ma gwamnatin kasar riyal biliyan 100, kimanin N10.3tr kenan domin fuskantar Corona.

A farkon shekarar 2018 ne Saudiyya ta kara kaddamar da harajin VAT, sa’annan ta rage kudin alawus da take biyan yan kasar, a kokarinta na karkatar da akalar tattalin arzikinta daga fetir.

Sai dai za’a iya samun bore daga jama’a game da matakan duba da cewa Coronavirus ta sa an rufe kasuwanci a kasar, kamar su Umrah, kasuwanni, sufurin jirgin sama da sauransu.

Duk da haka, ministan yace dole ne a dauki matakan don tara kudaden da za’a bukata don magance matsalolin da Coronavirus da zo dasu, musamman duba da karyewar man fetir.

Haka zalika gwamnatin ta soke wasu manyan ayyuka da take shirin gudanarwa tare da rage kudin wasu ayyukan duk domin cimma wannan manufa da ta sanya a gaba.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Liberia, George Weah ya sanar bude Masallatai da Coci-coci a kasar daga ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu a kokarinsa na dakile cutar Coronavirus.

Shugaba Weah ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda zai bude wuraren Ibada, amma ya kara wa’adin dokar ta baci a Monrovia, babban birnin kasar.

Sai dai ko da ya ayyana bude wuraren Ibadan, ya gindaya sharadi guda daya, wanda shine dole ne limaman Masallatai da coci su tabbata kashi 25 na jama’a kadai za su halarta don ibada.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel