Dalilin da yasa na janye jikina daga siyasar Najeriya – Goodluck Jonathan

Dalilin da yasa na janye jikina daga siyasar Najeriya – Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa ya janye jikinsa daga siyasa tun bayan faduwarsa zabe a shekarar 2015 ne don ya kula da gidauniyarsa.

Punch ta ruwaito Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu yayin da gwamnan Bayelsa, Duoye Diri ya rantsar da shuwagabannin jam’iyyar PDP a garin Yenagoa.

KU KARANTA: Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal

Jonathan yace yana janye jikinsa daga siyasa, amma kuma ya fahimci jama’a da dama basu fahimce shi ba, saboda basu gane muhimmancin matakin daya dauka a wajen sa ba.

Dalilin da yasa na janye jikina daga siyasar Najeriya – Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan
Source: Depositphotos

“Kada ku karaya idan baku ganni a wajen tarukan siyasa a jahar ba, da gangan na bayyana a wannan taro domin kada wasu fahimce ni a baibai. Ina janye jikina daga siyasa ne saboda gidauniyata, mutanen dake son hada kai da ni ba zasu yarda dani ba idan suka ga ina siyasa.

“Ina ganin tun da na jagoranci kasar nan a matsayin shugaban kasa, ya kamata na koma wasu fannoni inda za’a fi bukata ta, ta wannan hanya, zan iya taimaka ma kasata da ma jaha ta.” Inji shi.

Tsohon shugaban ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar su yi adalci a jagorancinsu, su yi kokari wajen hadin kan jama’a da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sa’annan tsohon shugaban ya yaba tare da jinjina ma gwamnan jahar, Douye Diri, bisa ga kyawawan halayen shugabanci da ya nuna zuwa yanzu.

Shi ma gwamnan, a nasa jawabin, ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar su dawo da duk yayan jam’iyyar da suka fice daga cikinta domin karfafa jam’iyyar a jahar.

“Allah ne Ya kawo mu wannan kujera, don haka kada mu yi ramuwar gayya, mu yafe ma kowa, kuma mu hada kai da kowa don cigaban jam’iyyarmu. Abu ne mai kamar wuya, amma zai yiwu saboda dukkaninmu yan uwan juna ne, don haka kada mu raba kawunanmu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel