COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar

COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar

Jamhuriyar Madagascar ta bukaci aiko da maganin gargajiyar da take amfani da shi wajen yaki da cutar coronavirus ga Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ana amfani da maganin wajen kariya da kuma maganin cutar.

Wakilan Najeriya sun garzaya kasar Equatorial Guinea inda za a karbo maganin tare da dauko shi zuwa Abuja.

Don saukake al'amarin sufuri, a raba kasashen Afrika zuwa yankuna inda Najeriya ta fada yankin Equatorial Guinea.

A daren jiya Lahadi ne Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 4,399 da muguwar cutar, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana.

COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar
COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar Hoto: The Nation
Asali: UGC

An samu sabbin karin masu cutar 81 a jihar Legas, jihar Jigawa ke biye mata baya da mutum 35 sai Borno da ke da 26.

Jihar Kano ta tabbatar da kamiwar karin mutum 26, jihar Bauchi ce mai mutum 20.

Amma kuma kungiyar masu hada magunguna da bincike ta Najeriya tara da kungiyar duba ingancin abinci da magani ta kasa ta bukaci a yi wa maganin Madagascar din gwajin inganci.

Har yanzu dai gwamnatin tarayya ba ta sanar da matsayarta ba don kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta tilasta wa hukumomin kula da cututtuka masu yaduwa na Afrika da su duba ingancin maganin gargajiyan.

KU KARANTA KUMA: Bala Muhammad ya rufe kananan hukumomi 3 a jahar Bauchi saboda Coronavirus

A makon da ya gabata ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ce ba a tabbatar da ingancin maganin ba.

Har ila yau, daga cikin matakan yakar COVID-19, kungiyar gwamnonin Najeriya ta fara tattaunawa da kungiyar likitocin Najeriya da kuma kungiyar malaman jinya kan yadda za a samo likitoci da ma’aikatan lafiya da za su bayar da gudunmawa.

Ma’aikatan lafiyan za su taimaka jihohin da lamarin ya yi barna a arewa maso yamma da arewa maso gabas musamman a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi, Yobe da kuma Borno.

Shugaban kungiyar gwamnonin, Dr. Kayode Fayemi, ne ke jagorantar tattaunawar da kungiyoyin kwararrun tare da wani tanadi mai tsoka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng