Daga yanzu takunkumi ya zama dole a Kano, masu kunnen kashi zasu je kurkuku - Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce daga yanzu saka takunkumin fuska ya zama wajibi a Kano tare da bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka samu suna saba doka.
Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da yake gabatar da jawabi a kan halin da jihar Kano ke ciki dangane da annobar korona.
Gwamnan Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa kotun tafi da gidanka guda 10 domin hukunta masu karya dokar kulle tare da bayyana cewa an saka dokar ne domin dakile yaduwar annobar a jihar.
"Ba wai haka kawai babu dalili mu ke yin haka ba. Mu na yin haka ne domin kare kanmu. Cutar nan yaduwa ta ke yi a tsakanin jama'a, hanya daya da za magance yaduwarta shine ta hanyar zama a gida, kauracewa taron jama'a, saka takunkumin fuska da biyayya ga sauran matakai," a cewar Ganduje.
A cewar gwamna Ganduje, gwamnati za ta samar da takunkumin fuska ga jama'a kyauta.
Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta hada kai da telolin cikin gida domin samar da isassun taunkumi ga jama'a.
Da ya ke gabatar da jawabi yayin taron, shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar Kano, Dr. Tijjani Hussain ya ce an gano ma'aikatan lafiya 47 sa suka kamu da cutar korona a makon da ya gabata.
Kazalika, ya ce ba a sake samun ma'aikatan lafiya da suka kamu da cutar ba a 'yan kwanakin nan.
Ya ce an samu wannan nasarar ne saboda kokarin gwamnatin jihar Kano na gaggauta bayar da kariya ga ma'aikatan lafiyan.
Hussain ya tabbatar da cewa mutum 576 aka tabbatar da suka dauke da cutar a jihar. An sallamin mutum 32 bayan an tabbatar da samun warakarsu.
DUBA WANNAN: Azumi da zafin rana ke kashe mutane a Jigawa - Sanata Ibrahim Hassan
"Daga cikin wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar a jihar Kano, an rasa rayukan mutum 21.
"A ranar Asabar, an samu mutum 84 wadanda ake zargin suna dauke da kwayar cutar. Hakan ya kai jimillar wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar a jihar Kano zuwa mutum 1,820," a cewarsa.
Kamar yadda NTA ta bayyana, ya ce kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar Kano ya samu kiran gaggawa 47 a ranar Asabar.
Jimillar kiran gaggawa da mu ka samu ya kai 1,313, "a tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi, 29 daga cikin samfur 84 da aka karba suna dauke da kwayar cutar.
"A halin yanzu mun karba tare da gudanar da gwaji a kan samfurin jinin mutane 2,072 a fadin jihar Kano," a cewar Dakta Hussain.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng