Kwamishina mai ci ya mutu a jihar Sokoto

Kwamishina mai ci ya mutu a jihar Sokoto

Kwamishinan kasa da gidaje, Surajo Gatawa, ya mutu da yammacin ranar Lahadi,kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito a daren nan.

Jaridar ta ce wata majiya a gidan gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar kwamishinan, sai dai ta ce majiyar ba ta bayar da karin bayani ba.

.Wata majiya ta sanar da TheCable cewa an yi jan'izarsa da misalin karfe 7:00 na dare a gidansa da ke kan titin Sama daura da Babban Tanki a Sokoto.

Marigayin na daya daga cikin kwamishinoni 26 da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya nada a watan Nuwamba, 2018.

Kwamishina mai ci ya mutu a jihar Sokoto
Marigayi Gatawa
Asali: Facebook

An fara nada shi a matsayin kwamishinan kimiyya da fasaha kafin daga bisani a mayar da shi zuwa ma'aikatar kasa da filaye.

DUBA WANNAN: Azumi da zafin rana ke kashe mutane a Jigawa - Sanata Ibrahim Hassan

Wannan shine karo na uku da gwamna Tambuwal ya rasa wani makusancinsa. Haruna Usman, kawun Tambuwal ya mutu ranar Alhamis.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, tsohon sanatan Najeriya daga jihar Adamawa, Paul Wampana, ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa Wampana ya mutu a cikin barcinsa da safiyar ranar Lahadi a gidansa Abuja, kamar yadda makusancinsa, Sylvester Ahmadu, ya shaidawa SaharaReporters.

Marigayin, wanda aka haifa a a garin Vimtim da ke karamar hukumar Mubi ta jihar Adamawa, ya taba rike shugaban majalisar dokokin tsohuwar jihar Gongola a jamhuriyya ta biyu.

Bayan kasancewarsa tsohon sanata mai wakiltar gabashin Adamawa, Wampana ya rike mukamin ministan lafiya lokacin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Shehu Shagari a shekarar 1983.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel