Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu

Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu

Ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ya warware jita-jitar da wasu jaridun yanar gizo ke yadawa a kan cewa shugaban JIBWIS, Sheik Bala Lau, ya mutu a daren ranar Asabar.

A cikin wani sako da ya wallafa a sahfinsa na 'Facebook', Pantami ya ce masu yada labarin basu samu bayaninsu daidai ba.

Pantami ya ce Sheikh Bala Lau yana nan da ransa, cikin koshin lafiya. Kazalika, ya nemi jama'a su yi watsi da duk wata jita-jitar cewa ya mutu.

A cewarsa, hotunan da ake yadawa na jana'izar Shaykh Adam Muhammad Gashua ne tare da yin fatan cewa kafafen yada labarai zasu gyara kuskuren da suka yi wajen sanarwar da suka fitar.

Jaridar SaharaReporters ta wallafa labarin cewa Sheik Bala Lau ya mutu ranar Asabar da daddare. Inda ta wallafa wasu hotuna da sunan na jana'izarsa ne da aka yi yau, Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Jama'a da dama sun nuna shakku a kan labarin na SaharaReporters.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa, ya sanar a shafinsa na tuwita cewa ya yi magana da Sheikh Lau bayan ganin labarin da SaharaReporters ta walla a kan cewa ya mutu.

Har ya zuwa wanna lokaci, SaharaReporters ba ta janye labarinta ko gyara kuskuren da ta yi ba, lamarin da yasa wasu ke zargin cewa da gangan suka yada labarin domin cimma wata manufarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel