Fadar Shugaban kasa ta ce ayi watsi da rade-radi a kan Farfesa Osinbajo

Fadar Shugaban kasa ta ce ayi watsi da rade-radi a kan Farfesa Osinbajo

- Fadar shugaban kasa ta yi magana game da rade-radin da ake yi a kan Yemi Osinbajo

- Mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasa ya ce Mai gidansa ya na nan

- Laolu Akande ya tabbatar cewa Farfesa Osinbajo ya na nan garau kuma ya na zuwa ofis

Fadar shugaban kasa ta maida martani a kan jita-jitar da wasu ke yi game da Farfesa Yemi Osinbajo, inda ta ta karyata rade-radi, ta kuma bukaci ayi watsi da labaran karyar.

Mai magana a madadin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande, ya ce mai gidansa ya na nan kalau a cikin koshin lafiya, bugu da kari ma ya na zuwa aiki a ofishinsa.

A ranar Asabar, 9 ga watan Mayu, 2020, Laolu Akande ya tabbatarwa jama’a halin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ke ciki a shafinsa na sadarwa na Instagram.

Mista Akande ya bukaci ‘yan Najeriya da: "Su cigaba da yin watsi da kwararrun makaryatan da su ke sharara labarin karya game da halin da mataimakin shugaban kasa ya ke ciki.”

Hadimin mataimakin shugaban kasar ya ke cewa: “Dinbin mutanenmu su na ganin mai girma shugaban kasa da mataimakinsa bini-bini a talabijin, su na jinsu a gidajen rediyo.”

KU KARANTA: Ana zargin Coronavirus da kashe mutum 300 a Jihar Bauchi

Bayan haka Bayin Allah su na bibiyar shugaban Najeriyar a kakafensu na sadarwa da yada labarai na zamani a yanar gizo inji babban hadimin ofishin mataimakin shugaban kasar.

Mai taimakawa mataimakin shugaban kasar ya kuma yi nuni da cewa mai girma Yemi Osinbajo ya jagoranci wani taro na kwamitin da ke kokarin gyara wutan lantarki a ranar Alhamis.

Farfesa Osinbajo shi ne shugaban wannan kwamiti na shugaban kasa wanda ke kunshe da gwamnan CBN, wasu gwamnoni da ministocin kudi da na wutar lantarki da wasu jami’ai.

Wadanda su ka halarci wannan taro da Yemi Osinbajo ta kafar yanar gizo sun hada da Mallam Nasir El-Rufai, Babatunde Fashola, Zainab Ahmed, da Godwin Emefiele inji Laolu Akande.

Har ila yau a ranar Juma’a 8 ga watan Mayu, Akande ya nuna hotonsa tare da Osinbajo lokacin da ya ke duba yadda makonsa ya kasance, ya na cewa za a shawo kan halin da aka shiga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel