Mutum daya ya mutu bayan gobara ta babbake asibitin masu jinyar korona

Mutum daya ya mutu bayan gobara ta babbake asibitin masu jinyar korona

- Gobara ta tashi a asibitin da ake ajiye masu jinyar cutar korona a Moscow, babban birnin kasar Rasha

- Hukumomi sun ce gobarar ta fara ne daga dakin wani mai jinyar cutar korona, amma za a zurfafa bincike

- Ya zuwa yanzu annobar cutar korona ta harbi kusan mutane 200,000 a kasar Rasaha tare da kashe mutane 1,800

Mutum daya ya mutu ranar Asabar bayan gobara ta tashi a asibitin masu jinyar cutar korona a Moscow, babban birnin kasar Rasha, kamar yadda hukuma ta tabbatar.

Asibitin, wanda ke yankin arewa maso gabashin birnin Moscow, an tsara shi ne a matsayin daya daga cibiyoyin lafiya da za a ke gudanar da gwajin cutar a babban birnin na kasar Rasha.

Ma'aikatar aiyukan gaggawa ta kasar Rasha ta sanar da kamfanin dillancin labarai na RIA cewa gobarar ta samo asaline daga dakin wani mai jinyar korona.

Ma'aikatar ba ta bayar da wani karin bayani ba bayan hakan, sai dai hukumomi sun ce an kashe wutar.

Mutum daya ya mutu bayan gobara ta babbake asibitin masu jinyar korona
Vladimir Putin; shugaban kasar Rasha da wani Likita
Asali: UGC

Sergei Sobyanin, wani jami'in hukuma a Moscow, ya sanar da cewa an kwashe dukkan sauran masu jinyar tare da mayar da su wani asibitin.

"Za mu gudanar da bincike mai zurfi a kan asalin gobarar," kamar yadda Sobyanin ya rubuta a shafinsa na tuwita.

DUBA WANNAN: Korona ta hallaka kwararren likita a jihar Borno

Tun a watan Maris kasar Rasha ta kulle birnin Moscow da sauran wasu sassan kasar bayan bullar annobar korona, wacce ya zuwa yanzu ta harbi kusan mutane 200,000 a kasar tare da kashe mutane 1,800.

Fiye da rabin mutanen da cutar korona ta kashe a kasar Rasha mazauna birnin Moscow ne, mai yawan mutane miliyan 12.7.

Adadin masu dauke da kwayar cutar korona a kasar Rasha ya yi tashin gwauron zabi fiye da na kasar Faransa da Jamus a cikin makon nan.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4151 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 745 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 128.

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 239 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel