Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Dan Iyan Kano, Alhaji Yusuf Bayero rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Dan Iyan Kano, Alhaji Yusuf Bayero rasuwa

Allah ya yi wa Dan iyan Kano, Alhaji Yusuf Bayero ya rasuwa.

Kafin rasuwarsa shine hakimin karamar hukumar Dawakin Kudu a jihar ta Kano.

Bayero ne hakimi na farko a karamar Ajingi a tarihin jihar Kano kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Dan Iyan Kano, Alhaji Yusuf Bayero rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Dan Iyan Kano, Alhaji Yusuf Bayero rasuwa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Allah ya gafarta masa zunubansa yasa Aljanna Makoma. Ameen.

DUBA WANNAN: COVID-19: Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe

In tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa mai bawa Gwamna Muhammadu Badaru shawara na musamman akan harkokin ilimin manya da na manyan makarantu, Ibrahim Ismail, rasuwa.

Marigayi Jarman Ringim kuma tsohon shugaban hukumar cigaban kananan hukumomi ya rasu ne a ranar Jumaa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin babban mataimaki na musamman ga maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a sabbin kafafan sadarwa, Auwalu D. Sankara a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi ta’aziyya ga daukacin al’ummar da ke masarautar Ringim bisa rasuwar Alhaji Ibrahim Ismail Jarman Ringim wanda ya rasu ranar Jumaa bayan fama da rashin lafiya da ya yi.

Alhaji Badaru da karshe yayi addua ga Allah subhanahu wata’ala da ya saka wa mamacin da aljanna firdausi kuma ya bai wa iyalan sa karfin gwiwar juriya da rashin da su kayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164