Ba Ajuri Ngelale ya fito da jawabin Shugaban kasa ba – Garba Shehu

Ba Ajuri Ngelale ya fito da jawabin Shugaban kasa ba – Garba Shehu

- Fadar Shugaban kasa ta yi magana game da wanda ya fito da jawabin Buhari

- Kwanakin baya jawabin Shugaban kasa ya shiga hannun jama’a kafin lokaci

- Garba Shehu ya ce zargin Ajuri Ngelale da fito da jawabin bai da gindin zama

Mai taimakawa shugaban kasar Najeriya wajen hulda da jama’a da yada labarai, Malam Garba Shehu ya kare abokin aikinsa, Mista Ajuri Ngelale daga zargin da wasu su ke jifansa da shi.

Kwanakin baya aka yi ta rade-radin cewa Ajuri Ngelale ne ya ke da hannu wajen fito da wani dogon jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya, ta bayan fage.

Malam Shehu ya musanya wadannan zargi, ya ce sam babu hannun Ajuri Ngelale. Mai magana da yawun bakin shugaban kasar ya ce babu wani cikin hadiman shugaban kasar da ake zargi.

Wata takarda mai kunshe da jawabin da shugaban kasar ya yi wa ‘yan kasa a game da annobar cutar COVID-19 ta fito ne tun kafin lokacin da aka shirya cewa shugaba Buhari zai yi magana.

KU KARANTA: Femi Adesina ya ce an kama wanda ya fallasa jawabin Buhari

"Abin takaici, an fara yi wa Ajuri Ngelale turnukun sharri, ana zargin abokin aikinmu wajen harkar yada labaran fadar shugaban kasa da fitowa Duniya da jawabin da shugaban kasa ya yi.

“Babu shakka masu yada wannan labarin karya su na da shirin karkatar da hankalin Ajuri ne yayin da ya ke kokarin fito da gwamnati, ya na wayar da kan ‘yan kasa a rediyo da talabijin."

Shehu ya bayyana Ngelale a matsayin mutum mai kwazo a fadar shugaban kasa. Ya kuma kara da cewa: “Babu wani ma’aikacin fadar shugaban kasa da ake zargi da yin wannan mugun aiki.”

Ajuri Ngelale ba ya cikin wadanda ke da hannu wajen shirya jawabin shugaban kasar. Shehu ya ce hadimin na Buhari bai da masaniya wajen tsara jawabin da mai gidan na sa ya yi a baya.

“Duk wasu bincikenmu sun nuna mana batun zargin Ngelale ba gaskiya ba ne. Akwai alamun rashin gaskiya tattare da shafukan yanar gizon da su ka fito da wannan labari.” Inji Shehu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel