Mun samu N697.5m na yaki da cutar COVID-19 – inji Fadar Shugaban kasa

Mun samu N697.5m na yaki da cutar COVID-19 – inji Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta ce mutane da kungiyoyi 111 ne su ka aiko da gudumuwarsu a cikin asusun bankunan da gwamnatin tarayya ta ware na yaki da cutar COVID-19 a Najeriya.

Mai taimakawa shugaban kasa wajen hulda da jama’a da yada labarai, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa sun samu kudi N697, 538, 108.00 kawo yanzu daga hannun Bayin Allah.

A wani jawabi da fadar shugaban kasar ta fitar ta bakin mai magana da yawun bakin shugaban kasar, ta ce takardun da su ke cikin ofishin babban akawun Najeriya su ka nuna wannan.

Shehu ya ce wasu sun rika bada har N5, N10, N14, da N20. Akwai kuma manyan attajirai da su ka bada gudumuwa mai tsoka, haka zalika akwai kamfanonin kasar da su ka yi hobbasa.

Kamfanin Dantata Property Development ya bada Naira miliyan 100. Kamfanin Ocean Trust Ltd ya bada Naira miliyan 25. Gidauniyar Ebele & Anyichuks Foundation ta bada miliyan 10.

KU KARANTA: COVID-19 ta kawo damar haramta Almajiranci a Arewa- Gwamna El-Rufai

Mun samu N690m na yaki da cutar COVID-19 – inji Fadar Shugaban kasa
Garba Shehu da Shugaban Najeriya Buhari a Daura
Asali: Twitter

Asibitin Nizamiya ya bada Naira miliyan 15. Kungiyar Full Gospel Business Men’s Fellowship ta bada Naira miliyan 10. Haka kuma kungiyar ‘yan kasuwan canji sun tara Naira miliyan 10.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa wadannan mutane da kungiyoyi da su ka bada gudumuwar kudi da kayan agaji ga kwamitin da aka kafa domin yaki da wannan mugun cuta.

A jawabin, shugaban kasar ya bayyana irin namijin kokarin da kamfanonin Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Guaranty Trust Bank, da kuma gidan jaridar This Day su ka yi.

Mai girma shugaban kasa ya yi kira ga sauran jama’a su yi koyi da wadannan mutane masu hali da su ka taimaka da kayan aiki da gina dakunan jinya da na yin gwaji a wasu jihohin kasar.

Gwamnatin tarayya ta tara wannan kudi ne daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa ranar 30 ga watan na jiya. Kwamitin yaki da COVID-19 ya na tara wadannan gudumuwa ne a wasu bankuna biyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel