COVID-19: Ma'aikatan lafiya biyu da almajirai 24 daga Kano sun sake kamuwa a Jigawa

COVID-19: Ma'aikatan lafiya biyu da almajirai 24 daga Kano sun sake kamuwa a Jigawa

- Gwamnatin jihar Jigawa ta ssanar da kamuwar ma'aikatan lafiya biyu da almajirai 24 da cutar korona a jihar

- Kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana, almajiran 24 da aka tabbatar da kamuwarsu na daga cikin wadanda jihar Kano ta mayar musu

- Ya ce akwai yuwuwar a samu karin ma'aikatan lafiya da suka kamu da cutar don a halin yanzu akwai wasu samfur da ba a samu sakamakonsu ba

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da kamuwar ma'aikatan biyu a jihar da cutar coronavirus.

Ta kara da cewa an samu karin almajirai 24 da aka dawo dasu daga Kano dauke da muguwar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Abba Zakari, ya sanar da manema labarai hakan a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayun 2020.

Ya ce ma'aikatan lafiya da suka kamu da cutar suna aiki ne a asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu da kuma asibitin kwararru na Rasheed Shekoni da ke Dutse.

Kamar yadda jaridar Premium times ta bayyana, akwai yuwuwar ma'aikatan lafiya da yawa sun kamu da cutar don sakamakon wasu yana kan hanya.

Zakari, wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar Jigawa, ya ce an sake diban samfur din almajirai 24 da aka dawo dasu daga Kano.

COVID-19: Ma'aikatan lafiya biyu da almajirai 24 daga Kano sun sake kamuwa a Jigawa

COVID-19: Ma'aikatan lafiya biyu da almajirai 24 daga Kano sun sake kamuwa a Jigawa. Hoto daga SaharaReporters
Source: UGC

KU KARANTA: Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

Wannan ci gaba abun firgici ne da tsoro saboda daga cikin samfur 607 na almajirai da aka dauka, 148 kadai aka yi wa gwaji. 40 daga ciki kuwa duk suna dauke da cutar, Zakari yace.

Akwai sama da almajirai 1,000 da aka killace a sansanin 'yan bautar kasa na Yakubu Gowon da ke Jigawa.

An diba samfur dinsu don tabbatar da ingancin lafiyarsu kafin a mika su ga iyayensu ko kuma cibiyar killacewa ta jihar.

Almajiran da aka killace sun hada da wadanda suka dawo daga jihohin Kano, Kaduna, Gombe, Nasarawa, Filato da sauransu.

Tuni aka mika wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar zuwa cibiyar killacewa ta jihar, jami'ai suka tabbatar.

A halin yanzu, jihar Jigawa na da jimillar mutum 85 da ke dauke da kwayar cutar kuma aka tabbatar. Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel