Kaduna: Mazauna wani kauye sun firgice bayan jirgin sama ya sako musu bam

Kaduna: Mazauna wani kauye sun firgice bayan jirgin sama ya sako musu bam

Mazauna kauyen Kabrasha da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun bar yankin bayan tashin bam da suke zargin an jefa musu ta jirgin sama.

Duk da ba a rasa ko rai daya ba, sun ce lamarin ya faru a ranar Alhamis. Wata coci da gidajen da ke yankin duk sun tarwatse, jaridar ThisDay ta wallafa.

Shugaban kungiyar ci gaba ta Gbagyi, Peter Aboki, ya bayyana hakan a wata tattaunawa.

Ya ce kafin tashin bam din, mazauna kauyen sun koka da yadda jirgin ke kaiwa da kawowa a yankin tare da wurga wasu abubuwa a cikin daji.

Ya ce sa'o'i kadan kafin tashin bam din, an ga wasu mazaje dauke da makamai kusan su 100 suna wucewa ta yankin.

Ya ce wasu daga ciki a kasa suke amma wasu suna kan babur. Ya kara da cewa wasu daga ciki na dauke da tuta yayin da sauran ke maganganu da harshen larabci.

Ya ce mazauna kauyen tare da dagacin duk sun tsere zuwa inda ba a sani ba saboda tsoro.

Aboki ya ce ba zai iya cewa 'yan ta'adda ne suka sako bam din ba, don zai yuwu jami'an tsaro ne ke bibiyar 'yan bindiga.

Kaduna: Mazauna wani kauye sun firgice bayan jirgin sama ya sako musu bam
Kaduna: Mazauna wani kauye sun firgice bayan jirgin sama ya sako musu bam. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

Kamar yadda yace, "Jirgin ya saba yawo a yankin tare da sako abubuwa. Amma bamu san ko mene ne yake sakowa ba.

"A jiya Alhamis da rana sai jirgin ya saki bam wanda ya tarwatsa cocin Assembly Of God tare da gine-ginen da ke kusa da shi. Mazauna kauyen da yawansu manoma ne kuma suna gona abin ya faru.

"Babu wanda ya rasa ransa amma bayan sa'o'i kadan sai ga mutane kusan 100 sun wuce dauke da makamai. Wasu na tafe a kasa amma wasu na kan babura."

Ya kara da cewa, "Daya daga cikinsu na dauke da tuta wacce ba ta Najeriya ba. Daya kuma na surkulle da harshen larabci.

"Mun zargi cewa tutar na iya zama ta 'yan ta'adda. Duk wanda zai dauka tuta da ba ta Najeriya ba, toh akwai wata ma'ana daban.

"Mutane sun bar kauyen don har dagaci ya tsere kauyen Gwagwada."

Mohammed Jalige, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna bai amsa wayar da aka dinga kiransa ba don jin karin bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel