Yanzu-yanzu: Korona ta sake kama mutum 13 a Nasarawa

Yanzu-yanzu: Korona ta sake kama mutum 13 a Nasarawa

- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya sanar da cewa an samu sabbin mutum 13 da suka kamu da korona a jihar

- Ya ce hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta dauka samfur din mutum 78 amma 13 daga ciki sun tabbata da cutar

- Gwamna Abdullahi Sule ya ce daga cikin sabbin masu dauke da cutar akwai matafiya daga jihohin Legas da Kano

Sabbin mutum 13 ne aka tabbatar suna dauke da cutar korona a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya.

Tara da cikin sabbin mutum 13 duk matafiya ne da suka dawo daga jihohin Lagos da Kano, jaridar SaharaReporters ta wallafa.

Wannan ne ya kai jimillar masu cutar a jihar zuwa 25 da kuma mutuwar mutum daya.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bada wannan sanarwar a ranar Juma'a yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta karba samfur din mutum 78 amma 13 ne aka tabbatar suna dauke da cutar.

Ya kara da cewa, mutum huda daga cikin 13 duk sun samu cutar ne bayan ma'amala da suka yi da marigayi dana majalisar jihar, Suleiman Adamu, wanda cutar korona ta kashe.

Yanzu-yanzu: Korona ta sake kama mutum 13 a jihar Nasarawa
Yanzu-yanzu: Korona ta sake kama mutum 13 a jihar Nasarawa. Hoto daga SaharaReporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Yadda aka yi min maganin korona – Shugaban kwamitin kar ta kwana

A wani labari na daban, Farfesa Abdulrazak Habib, Shugaba a kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a Kano, ya bayyana irin halin da ya shiga bayan kamuwa da korona da kuma yadda aka masa magani ya warke.

A ranar Alhamis 7 ga watan Mayu ne aka sallami Habib da wasu mambobin kwamitin na kar ta kwana da suka kamu da cutar tun ranar 17 ga watan Afrilu bayan sun warke.

Farfesan da ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da Jamiar Bayero ya ce an bashi magunguna da yawa da suka hada da "ruwan magani da aka saka masa ta jijiyoyi, iskar oxygen da siracen habbatus sauda da aka rika shaka masa, shayin chitta da wasu abubuwan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel