Yanzu-yanzu: FG ta sakar wa malaman jami'a masu yajin aiki albashi

Yanzu-yanzu: FG ta sakar wa malaman jami'a masu yajin aiki albashi

Malaman jami'o'i da suka tafi yajin aiki a kan sabon tsarin biyan albashi, sun samu albashinsu da gwamnatin tarayya ta rike a yau Juma'a 8 ga watan Mayun 2020.

An gano cewa malaman jami'o'in na bin bashin albashi tun daga na watan Fabariru har zuwa na watan Afirilu, saboda sun ki shiga sabon tsarin gwamnatin tarayya.

A watan Maris ne kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i suka bayyana tafiyarsu yajin aiki tun bayan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hana mambobin ta albashi.

A yayin sassauta hukuncinsa, Shugaba Buhari ya bada umarnin sakin albashin malaman makarantar, jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

Amma kuma, har a halin yanzu ba a sani ba ko dukkan malaman sun bi umarni ta hanyar shiga sabon tsarin ko kuma rangwame aka yi musu haka kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel