Baƙin ciki ya tunkaro jihohin Najeriya yayin da lalitar gwamnatin tarayya ta yi kasa

Baƙin ciki ya tunkaro jihohin Najeriya yayin da lalitar gwamnatin tarayya ta yi kasa

Ministar kudin Najeriya, Hajiya Zainab Ahmed, ta fayyace girman karayar tattalin arziki da ke tunkaro kasar a sanadiyar annobar korona da ta yi wa duniya daurin dabaibayi.

Dukkanin matakan gwamnatin kasar, za su tafka gagarumar asara a sanadiyar mummunan tasirin da annobar korona za ta yi wa hasashen da suka yi a kan kudaden shiga da za a samu a bana.

Akwai yiwuwar gwamnatin jihohi da dama ba za su iya sauke muhimman nauye-nauyen da suka rataya a wuyansu da suka hadar har da biyan albashin ma'aikata, a sanadiyar raguwar kudaden shiga da za su samu daga lalitar gwamnatin tarayya.

Jihohin da suke tsammanin raba Naira tiriliyan 3.3 a tsakanin a wannan shekara, ba za su samu abin da ya haura naira tiriliyan 2.1 ba kamar yadda ministar kudin ta yi hasashe.

Kananan hukumomin wadanda ke sa ran raba Naira tiriliyan biyu da rabi, ba za su samu sama da Naira tiriliyan 1 daga asusun gwamnatin tarayya ba.

Haka kuma gwamnatin tarayya wadda ta yi hasashen za ta tashi da kasafin naira tiriliyan 4.8, a yanzu abin da za ta samu bai wuce naira tiriliyan 2.4 ba.

Wannan shi ne ya kasance kaso 50 cikin 100 na kudaden da gwamnatin tarayya ta yi tsammanin samu kamar yadda ministan ta bayyana.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa; Zainab Ahmed
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa; Zainab Ahmed
Asali: Depositphotos

Hajiya Zainab ta fadi hakan ne yayin taron tattaunawa da 'yan kasa, wanda ma'aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa ta shirya tare da hadin gwiwar ma'aikatar ci gaban kasa-da-kasa ta Birtaniya, DFID.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, an gudanar da taron na karawa juna sani dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka biyo bayan karyewar farashin man fetur a kasuwar duniya da annobar korona ta yi sanadi.

Ta ce an samu ragi ba kadan ba a tsinkayen da gwamnatin ta yi na kudaden shiga da ta yi tsammanin samu daga makamashin man fetur da iskar gas, hukumar kwastam, da kuma kudin harajin kaya wato VAT.

KARANTA KUMA: Duk da matsin lamba, ba za mu yi karyar bullar cutar korona ba a jihar Kogi - Dr Haruna

A cewarta, duka duka dai naira tiriliyan 8.6 gwamnatin tarayya ta yi tsammanin za su shigo lalitar a shekarar 2020, sai kuwa a yanzu abin da take tsammani bai wuce naira tiriliyan 3.3 ba.

An samu ragi na kudaden shiga da hukumar hana fasa kwauri ta yi tsammani daga naira tiriliyan 1.5 zuwa naira tiriliyan 1.2, haka kuma za a samu ragi a kudin harajin kaya da ya fado zuwa naira tiriliyan 2 daga naira tiriliyan 2.1 da aka kiyasta.

Mafi munin karayar tattalin arziki da za a fuskanta a Najeriya shi ne a sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.

A kasafin kudin kasa na bana, gwamnatin Najeriya ta kiyasta farashin man fetur a kan dala 55 duk ganga, inda bayan ta sake nazari ta yi kiyasin farashinsa a kan dala 30.

A yanzu kuwa farashin kowace ganga ta danyen man fetur irin nau'in na Najeriya bai kai dala 20 ba a kowace ganga daya.

Ministar ta ce "muna ganin daga watan Yunin 2020, jihohi za su fara fuskantar karancin shigowar kudi da durkushewar tattalin arziki musamman kalubale wajen biyan albashin ma'aikata, wanda tun a yanzu ya kamata a tashi su farga domin daukan matakai."

Sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun hadar da; karamin ministan kudi; Prince Clem Agba, shugaban ofishin kasafi da tsare-tsaren kasa; Mr. Ben Akabueze, da kuma babban jami'i na majalisar tattalin arzikin Najeriya, Lade Jaiyeola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel