Cutar korona gaskiya ce – Babban malamin Musulunci

Cutar korona gaskiya ce – Babban malamin Musulunci

Babban limamin masallacin Yelwa da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Filato, Malam Abdulkareem Salihu, ya ce annobar Coronavirus da ta addabi duniya ba karya bace.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kiyaye duk wasu dokokin hana yaduwar cutar.

Imam Salihu ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da aka yi da shi a garin Filato.

Malamin addinin Musuluncin ya ce: "Babu shakka a kan wanzuwar cutar coronavirus. Cutar gaskiya ce kuma bai kamata jama'a su dauketa da wasa ba ko su karyata wanzuwarta.

"Babbar yaudarar kai ce mutum ya musanta wanzuwar annobar nan."

Cutar korona gaskiya ce – Babban malamin Musulunci
Babban malamin Musulunci ya ce cutar korona gaskiya ce Hoto: Brookings
Asali: UGC

Malam Salihu ya jaddada cewa Allah mai girma da daukaka ya yi bayanin cewa za a jarabci dan Adam da cutuka daban-daban ko yunwa.

Ya ce wannan lokacin babbar jarabawa ce a fadin duniya kuma zai fi idan aka koma ga Allah tare da neman yafiya da gafara.

Malamin ya kara da kira ga gwamnatocin jihohi da tarayya da su tallafawa jama'a da abinci ballantana a lokacin nan da aka hana jama'a fita.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa Orji Kalu na shekaru 12 a gidan yari

"Duk da dokar hana zirga-zirga babbar hanya ce ta dakile yaduwar cutar, akwai bukatar gwamnati ta samar da hanyar rage radadi ga jama'a.

"Ina kira ga duk wanda yake jihadin nan da ya kiyaye dokokin gwamnati na kariya. Ina kara kira ga kowa da mu yi amfani da watan Ramadana don addu'ar Allah ya yaye mana wannan annobar," ya kara da cewa.

A gefe guda, mun ji cewa a kalla mutum 155 aka gano sun rasu a jihar Yobe a kwanaki shida da suka gabata bayan bayyanar alamar annobar Coronavirus.

Mace-macen da ke faruwa a garin Gashua da Potiskum sun janyo tsoro a zukatan jama'ar jihar don yanayin hakan ne ya fara a jihar Kano.

Wani mazaunin jihar wanda ya yi magana da jaridar New Telegraph, ya ce a makon da ya gabata an samu rashin rayuka 98 a Potiskum yayin da 57 suka rasu a Gashua.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel