An sallami masu jinyar korona 16 baya sun warke sarai a Kano
Labarin da Legit.ng ke samu daga shafin tuwita na Ibrahim Isah (@ibrahimisahTVC) wakilin gidan talabijin na TVC a jihar Kano, na nuni da cewa an sallami mutane 16 da ke jinyar cutar korona bayan sun warke sarai.
Daga bisani kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammed Garba, ya tabbatar da sallamar mutanen a cikin wani jawabi da ya fitar.
Kwamishinan ya ce daga cikin mutanen da aka sallama akwai Farfesa Abdulrazak Garba Habeeb na sashen koyar da aikin likita a jami'ar Bayero da kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.
A ranar Laraba ne Legit.ng da sauran kafafen yada labarai suka sanar da cewa an sallami mutum uku da ke jinyar cutar covid-19 bayan sun warke a jihar Kano, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta jihar ta sanar a ranar Laraba.
DUBA WANNAN: Garkameku zamu kara yi idan kuka cigaba da cunkushewa - FG
Wanda kuma shine karo na farko da aka samu labarin warkewar wani mai dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya a Kano ta fitar ranar Laraba a shafinta na tuwita.
A ranar Talata ne kwamitin shugaban kasa na kar ta kwana a kan annobar covid-19 (PTF) ya yi gargadi a kan ajiye ma su dauke da kwayar cutar korona da su ke da koshin lafiya a cibiyar killacewa.
Jagoran PTF, Dakta Sani Aliyu, ya shawarci gwamnatocin jihohi a kan kwantar da duk wani mai dauke da kwayar cutar korona, inda ya bayyana cewa zai fi dacewa a jiye kaso 80 na ma su dauke da cutar a wurare ma su kyau kamar Otal.
Dakta Aliyu ya bayar da wannan shawara ne ranar Laraba yayin taron da kwamitin PTF ya saba gudanarwa da manema labarai a kowacce rana.
Kazalika, ya shawarci jihohi su fara shiri na musamman a cibiyoyinsu na killacewa tare da samar da gadajen kwanciya da yawansu kar ya gaza 300.
Ya bayyana cewa ma su dauke da kwayar cutar da ba su galabaita ko nuna wasu alamun tsananin rashin lafiya ba, ba sa bukatar dawainiya mai yawa, kawai sa mu su ido za a yi da saka mu su wasu ka'idoji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng