Masari ya nada manyan Alkalan kotunan shari’ar Musulunci 2, da wasu guda 2

Masari ya nada manyan Alkalan kotunan shari’ar Musulunci 2, da wasu guda 2

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya nada sabbin alkalai guda hudu na kotunan jahar Katsina a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Daily Trust ta ruwaito a yayin da yake rantsar dasu, gwamnan ya yi kira a gare su dasu kasance masu tsantseni, gaskiya da rikon amana wajen gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu.

KU KARANTA: Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi

Alkalan da aka nada sun hada da Safiya Badamasi Umar SAN da Barrister Ashiru Sani a matsayin Alkalan babbar kotun jahar.

Sai kuma Mohammad Makiyyu Adam da Adam Salihu Yarima a matsayin Alkalan kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci.

Masari ya nada manyan Alkalan kotunan shari’ar Musulunci 2, da wasu guda 2
Mai sharia Safiya Badamasi SAN Hoto: TheNigerianLawayer
Asali: UGC

Masari ya bayyana musu cewa nadin nasu na tattare da hakkoki masu nauyi a wuyansu dake bukatar kwarewa da sadaukar da kai wajen sauke su, tare da tsoron Allah wanda shi ne a gaba.

Gwamna Masari yace manufar kowanne ma’aikacin shari’a shi ne tabbatar da adalci da gaskiya, wanda shi ne tushen samar da zaman lafiya da mulki nagari.

“Bangaren sharia na fuskantar kalubale da dama a wannan lokaci, daga ciki har da jan kafa da ake samu wajen kammala shari’u, don haka akwai bukatar yi ma tsarin garambawul don tabbatar da samar da adalci a jahar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Tsohon babban Alkali, Mai Sharia Dahiru Saleh, matawallen masarautar Katagum ya rasu a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Jaridar TheCable ta ruwaito Alkali Dahiru Saleh ya taba zama shugaban babbar kotun babbar birnin tarayya Abuja, ya rasu ne a garin Bauchi, amma za’a yi jana’izarsa a garin Azare.

Marigayi Dahiru shi ne Alkalin da ya yanke hukuncin soke zaben shugaban kasa na June 12 1993, zaben da marigayi Cif MKO Abiola yayi ikirarin lashewa a zamanin mulkin Janar IBB.

Masana siyasa na ganin ba’a taba yin zaben gaskiya da gaskiya kamar na June 12 1993 ba, inda Abiola na jam’iyyar SDP ke kan gaba da Bashir Tofa na jam’iyyar NRC, da tazara mai yawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel