Wata ‘yar Najeriya ta bayyana yadda take gwagwarmaya da cutar korona, ta ce ba ta iya numfashi

Wata ‘yar Najeriya ta bayyana yadda take gwagwarmaya da cutar korona, ta ce ba ta iya numfashi

- Wata mata mai suna Chychy Chukwu ta bayyana yadda take fama da cutar coronavirus ta Twitter

- Matar ta ce duk da NCDC ta dauketa zuwa cibiyar killacewa, tana cikin tsananin ciwo

- Kamar yadda tace, numfashinta koda yaushe barazanar daukewa yake don ji take kamar ta kashe kanta

Wata mata 'yar Najeriya mai suna Chychy Chukwu ta bayyana yadda take fama da cutar korona a shafinta na Twitter.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, a ranar Litinin 4 ga watan Mayu ne NCDC ta zo ta tafi da ita cibiyar killacewa. Ta ce duk da an dauka samfur din ta kuma alamun cutar sun bayyana, tana fatan a ce mata ba cutar bace.

Matar ta kara da bayyana tsananin ciwon da take ciki don har numfashinta kokarin kubcewa yake. Tana ji tamkar ta kashe kanta.

"NCDC sun dauke ni jiya zuwa cibiyar killace masu cutar coronavirus, National hospital. An dauki samfurina kuma ina fatan ace bana dauke da cutar. Amma, radadin mai tsanani ne, bana iya numfashi. Radadin na durkusar dani. Ina son kawo karshen rayuwata,” ta rubuta a twitter.

Wata ‘yar Najeriya ta bayyana yadda take gwagwarmaya da cutar korona, ta ce ba ta iya numfashi

Wata ‘yar Najeriya ta bayyana yadda take gwagwarmaya da cutar korona, ta ce ba ta iya numfashi Hoto: Chychy Chukwu
Source: Twitter

A wani labari na daban, wata mata mai suna Oluwaseun Ayodeji ta bada labarin yadda ta warke daga cutar korona.

A takaitaccen bidiyon, matar ta yi kira ga marasa cutar da su guji nuna kyama ga masu cutar.

Ta ce a karon farko da aka sanar da ita tana dauke da muguwar cutar ta shiga tsananin rudani.

KU KARANTA KUMA: An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano

A cewarta, duk da babu takamaiman bayani a kan kariya daga cutar, akwai bukatar a kiyaye tsafta tare da daina shiga cunkoso.

Har ila yau a wani labarin mun ji cewa yara Almajirai 16 da gwamnatin jihar Kano ta mayar jihar Jigawa suna dauke da kwayar cutar Coronavirus, gwamnatin Muhammadu Badaru Talamiz, ta sanar.

Kwamishana lafiyan jihar, Abba Zakari, ya bayyana hakan ne a hirar da ya shirya a shafin Facebook dinsa inda yace cikin samfur 45 da aka tura gwaji, 16 na dauke da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel