Annobar korona ta bulla gidan gwamnatin Legas, ta kama mutane 10
Kwamishinan lafiya na Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin ma'aikatan fadar gwamnatin jihar su 10.
Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na tuwita (@ProfAkinAbayomi), kwamishinan ya ce gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da matarsa, Joke Sanwo-Olu, basa dauke da kwayar cutar, kamar yadda sakamakon gwajinsu ya sha nunawa.
Ya yi kira ga mazauna jihar Legas da su cigaba da rungumar amfani da takunkumi tare da yin biyayya ga dukkanmatakan dakile yaduwar annobar da suka hada da nesanta, wanke hannu da kula da tsaftar jiki.
"Dukkan matakan da aka saka yayin sassauta dokar kulle suna nan daram, zasu cigaba da aiki. Alhakin kowanne mutum ne ya tabbatar da cewa an dakatar da yaduwar annobar a jihar Legas," a cewarsa.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wasu manyan mutane uku da suka yi suna sun mutu a cikin sa'a 24 daga cutar da ake zargin cewa annobar korona ce jihar Yobe, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.
Manyan mutane sune; tsohon mamba mai wakiltar Nguru/Machina/Karasuwa/Yusufari a majlisar wakilai ta kasa, Alhaji Baba Bukar Machina, Muazu Buraji, darektan ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe, da Alhaji Bana Kura, wani sanannen ma'aikacin gwamnati a Geidam.
DUBA WANNAN: Kaso 80 na ma su cutar korona babu bukatar a kwantar da su a asibiti - Shugaban PTF
Machina ya mutu ne a cibiyar killacewa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kuma za a binne shi ranar Alhamis.
Da SaharaReporters ta tuntubi Mamman Mohammed, darektan yada labarai da kafafen sadarwa a Yobe, ya ce bashi da masaniya a kan abinda ya ke faruwa,
Ya bayyana cewa kwamishinan lafiya na Yobe zai gabatar da jawabi ga manema labarai a kan halin da ake ciki a jihar.
A ranar Laraba ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa a kalla mutum 155 ne su ka mutu a cikin kwanaki 6 a kananan hukumomin Gashua da Potiskum da ke jihar Yobe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng