Amfani da Chloroquine: Duk lalube muke yi a cikin duhu – Gwamnan Bauchi

Amfani da Chloroquine: Duk lalube muke yi a cikin duhu – Gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya ce baya shayin kowa game da goyon bayan da ya bayar na yin amfani da Chloroquine da Zithromax don maganin Coronavirus a jahar.

Punch ta ruwaito gwamnan ya ce a matsayinsa na tsohon mai cutar Coronavirus, ya yi amfani da maganin wajen samun waraka, amma ya ce daga karshe Allah ne Ya warkar da shi.

KU KARANTA: Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don yaki da Corona – Ministan Lafiya

Sai dai ko da gwamnan yake goyon bayan amfani da magungunan biyu, ya bayyana cewa shi bai ce mara lafiya ya dinga amfani da maganin yadda ya so ba, ba tare da shawarar likita ba.

Amfani da Chloroquine: Duk lalube muke yi a cikin duhu – Gwamnan Bauchi
Gwamnan Bauchi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

“Game da maganan da na yi a kan amfani da Chloroquine, Zinc, Zithromax, da Vitamin C don maganin Coronavirus, an canza min magana, na yi fama da cutar nan, amma ta yaya na warke?

“Na bayar da shawara ne kawai, ba shawarar kwamitin jahar Bauchi dake yaki da cutar Coronavirus bace, don haka bana shayin kowa don na ce na yi amfani da magungunan wajen samun sauki, Allah ne Ya warkar da ni.

“Ba lallai bane sai Chloroquine, kasashe da dama na amfani da magunguna daban-daban, kowa ya sani COVID19 ba shi da magani, lalube kawai muke yi a duhu, amma idan har ka fara samun alamun cutar, sha Chloroquine, za ka warke.” Inji shi.

A wani labarin, Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa a shirye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take ta amince da maganin gargajiya don yaki da Coronavirus.

Daily Nigerian ta ruwaito Ehanire ya bayyana haka ne a ranar Talata,yayin da kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar, PTF, take yi ma yan majalisa jawabi game da ayyukansu.

Sai dai Ministan ya ce amma fa dole ne maganin gargajiyan ya samu tantancewa tare da amincewa daga cibiyar binciken magunguna da cigabansu ta Najeriya, NIPRD.

A cewar ministan, duk wani boka ko mai maganin gargajiya da ya yi ikirarin gano maganin Coronavirus ya tafi NIPRD don samun takardar amincewa kafin a yi gwajin maganin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng