Yadda aka sha tataburza tsakanin 'yan uwa da kwamitin yaki da annobar covid-19 a kan gawar mahafiyar Buratai

Yadda aka sha tataburza tsakanin 'yan uwa da kwamitin yaki da annobar covid-19 a kan gawar mahafiyar Buratai

An samu 'yar hatsaniya tsakanin 'yan uwanTukur Buratai, babban hafsan rundunar soji, da kwamitin yaki da annobar covid-19 a jihar Borno a kan sakin gawar mahaifiyarsa, kamar yadda jaridar Thecable ta rawaito.

TheCable ta rawaito cewa Kakah Hajja, mahaifiyar Buratai, ta mutu ranar Talata daga annobar cutar covid-19.

Wata majiya a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH) ta ce sakamakon gwaji ya nuna cewa Hajja ta na dauke da kwayar cutar covid-19.

Umar Kadafur, mataimakin gwamnan Borno wanda shine shugaban kwamitin yaki da covid-19 a jihar, ya sanar da dangin Buratai cewa akwai ka'idoji da ake bi kafin sakin gawar wanda korona ta hallaka.

Sai dai, dangin na Buratai sun ki amincewa da mataimakin gwamnan, lamarin da ya haddasa cacar baki mai zafi a tsakani, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

"Ibrahim Buratai, wanda ya jagoranci sauran 'yan uwansa zuwa asibitin, ya kafe a kan cewa sai an sakar musu gawar mahaifiyarsu, wacce ya ce ta shafe fiye da wata uku tana fama da rashin lafiya, a saboda haka ba zai yiwu a ce annobar covid-19 ce ta kasheta ba.

"Shi ma mataimakin gwamna ya kafe a kan cewa sai an bi ka'ida, wacce ta hana mika gawar wanda covid-19 ta hallaka ga danginsa," a cewar majiyar TheCable.

Yadda aka sha tataburza tsakanin 'yan uwa da kwamitin yaki da annobar covid-19 a kan gawar mahafiyar Buratai
Marigayiya Kakah Hajja
Asali: UGC

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta fitar da jerin wasu matakai da sai an bisu kafin a saki gawar wanda ya mutu sakamakon annobar covid-19.

Daya daga cikin matakan shine tabbatar da cewa ma'aikatan lafiya sun kammala wasu hikimomi a kan gawa kafin sakinta ga dangin mamaci.

DUBA WANNAN: Fitattun manyan mutane uku da suka mutu cikin sa'a 24 a jihar Yobe

Sai dai, dangin Buratai sun bukaci a basu gawar marigayiya Hajja nan take bayan mutuwarta.

Lamarin ya yi zafin da cacar baki a kai ga bawa hammata iska a tsakanin jami'an tsaron mataimakin gwamna da wasu dakarun soji da suka raka 'yan uwan Buratai zuwa asibitin.

"Sai da mataimakin gwamna da wani babban jami'in soja suka shiga lamarin kafin a sakarwa 'yan uwan Buratai gawar Hajja, wacce tuni aka binneta a makabartar Maimalari da ke Maiduguri," a cewar majiyar TheCable.

Da TheCable ta tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Bakura Abba, ya ce bashi da masaniyar cewa hakan ta faru.

TheCable ta ce kakakin rundunar soji, Sagir Musa, bai amsa kiransu ko bayar da amsar sakon da suka aika masa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel