Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don yaki da Corona – Ministan Lafiya

Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don yaki da Corona – Ministan Lafiya

Ministan kiwon lafiya, Mista Osagie Ehanire ya bayyana cewa a shirye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take ta yi amince da maganin gargajiya don yaki da Coronavirus.

Daily Nigerian ta ruwaito Ehanire ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar, PTF, take yi ma yan majalisa jawabi game da ayyukansu.

KU KARANTA: Buhari ya yi ma mai martaba Sarkin Daura addu’ar samun lafiya

Sai dai Ministan ya ce amma fa dole ne maganin gargajiyan ya samu tantancewa tare da amincewa daga cibiyar binciken magunguna da cigabansu ta Najeriya, NIPRD.

A cewar ministan, duk wani boka ko mai maganin gargajiya da ya yi ikirarin gano maganin Coronavirus ya tafi NIPRD don samun takardar amincewa kafin a yi gwajin maganin.

Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don yaki da Corona – Ministan Lafiya
Ministan Lafiya
Asali: Twitter

“A da an ce Chloroquine na kashe kwayar cutar Coronavirus, amma har yanzu ana kan gwaji game da haka. Muma sai mun gwada magungunan gargajiyan kafin mu tabbatar da ingancinsu wajen kashe kwayar cutar, da kuma gano ko yana da illa ga jikin dan Adam.

“Don haka aikin cibiyar ce ta gudanar da tantancewa a kan magungunan kafin a gwada su.” Inji shi.

Daga karshe Ministan ya gargadi jama’a daga amfani da magungunan gargajiya a yanzu, domin kuwa hakan ka iya bude kofar wata sabuwar annobar a kasa.

A wani labarin kuma, Gwamnatin kasar Japan ta shirya sanar da maganin Remdesivir a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu a matsayin maganin cutar Coronavirus.

Gwamnatin Japan ta ce baya ga amfani da Remdesivir wanda kamfanin Gilead ta sarrafa shi a matsayin maganin cutar, za ta amince da maganin Avigan ma a wannan watan.

Remdesivir wanda asali an samar da shi ne don maganin cutar Ebola, amma bayan gwaji a kan masu Coronavirus ya nuna yana rage tsawon lokacin da ake dauka kafin a warke daga cutar.

Shi kuma maganin Avigan an samar da shi ne a kamfanin Fujifilm Toyama Chemical na kasar Japan, kuma za’a amince da shi idan har ya yi aiki a kan marasa lafiya guda 100.

Sunan maganin Avigan Favipiravir, kuma a shekarar 2014 aka amince da shi a Japan don maganin mura, musamman muran da basu da magani a kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel