Coronavirus: Kano ta sake samun karin mutum biyar da suka mutu

Coronavirus: Kano ta sake samun karin mutum biyar da suka mutu

A ranar Alhamis ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da karin mutuwar majinyata 5 da ke fama da cutar coronavirus a jihar.

A wani rubutu da aka wallafa a shafin Twitter na ma'aikatar lafiyar, ta tabbatar da sallamar wasu mutum uku da suka warke daga cutar.

Mutuwar mutum biyar din an sanar da ita ne da safiyar Alhamis kamar yadda NCDC ta sanar a daren ranar Laraba.

NCDC ta sanar da mutuwar mutum biyar da ke fama da cutar coronavirus a fadin kasar nan, lamarin da ya kai jimillar mamatan zuwa 103.

Amma kuma, NCDC bata sanar da jihohin da aka samu mutuwar ba.

A takardar da ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta fitar, ta ce a halin yanzu jihar Kano na da mutum 427 da ke dauke da cutar kuma aka tabbatar.

Majinyata 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar yayin da aka sallama shida bayan sun warke.

A halin yanzu, kungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta tabbatar da kamuwar ma'aikatan jinya 18 da muguwar cutar a jihar Kano.

Kungiyar likitoci ta kasa kuwa tuni ta sanar da kamuwar likitoci 34 da ke aiki a asibitoci daban-daban na fadin jihar.

KU KARANA KUMA: COVID-19: WHO ta kara samar da jami'ai 88 a Kano

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar hana walwal a jihar don hana yaduwar cutar, Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanar da cewa za a dinga dage dokar a dukkan ranakun Litinin da Alhamis don samun zuwa kasuwa.

Wannan sanarwa ta taho tare da wasu matakai masu tsauri na kiyaye nisantar juna da saka takunkumin fuska a duk lokacin fita.

Hakazalika, kasuwannin abinci ne kadai za a dinga budewa.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ja kunnen jihar a kan gaggawar da tayi wajen dage dokar a yayin da annobar ke ganiyarta a jihar.

Sun ce koda za a dage dokar, akwai bukatar nisantar juna tare da tsaftace kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel