Yanzu-yanzu: An sallami karin mutane 37 da suka warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami karin mutane 37 da suka warke daga Coronavirus

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-olu, ya sanar da labarin sallamar masu jinyar cutar Coronavirus 37 yau Laraba, 6 ga watan maris, 2020 a jiharsa kadai.

Sakataren yada labaran gwamnan, Gboyega Akosile, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita da yamman nan.

Ya ce mutane 37 da aka sallama sun hada da maza 19 da mata 18. Dgaa cikinsu akwai dan kasar Indiya daya.

Kawo yanzu, jihar Legas ta sallami mutane 358 da tayi jinya a asibitocinta da cibiyoyin killacewa.

An yi jinyansu ne a cibiyoyin killace masu cutar Korona na unguwanni Yaba, Onikan, Eti -Osa.

Jihar Legas ce tafi adadin masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya da mutane 1226.

Yanzu-yanzu: An sallami karin mutane 37 da suka warke daga Coronavirus
Yanzu-yanzu: An sallami karin mutane 37 da suka warke daga Coronavirus
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An harbi DPO, an kashe mutane 5, an sace shugaban karamar hukuma a Katsina

A bangare guda, gwamnatin jihar Kano ta sanar da sallamar mutane uku daga cibiyar killacewanta bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun samu waraka daga cutar ta Korona.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus na jihar, Dr Tijjani Ibrahim, ya bayyana hakan yayinda hira da manema labaran kwamitin.

Kawo yanzu, jihar Kano ta zarcewa birnin tarayya Abuja a yawan masu dauke da cutar ta COVID-19. Hukumar NCDC ta tabbatar da cewa mutane 365 suka kamu a Kano.

Wannan shine karo na farko da jihar Kano za ta sallami wasu cikin masu jinyar cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel