Jami'in tsaro sun kama matafiya da almajirai 150 a Kaduna

Jami'in tsaro sun kama matafiya da almajirai 150 a Kaduna

- An kama matafiya 150 da suka hada da almajirai a manyan motocin uku a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

- Matafiyan dai suna kokarin shiga jihar Kaduna ne daga babban birnin tarayya da kuma Nyanya da ke Nasarawa

- An kama almajiran ne a kananan hukumomin Soba da Giwa na jihar

A kalla matafiya 150 da suka hada da almajirai aka kama a manyan motocin uku a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a yau Laraba.

An kama sune suna kokarin shiga jihar Kaduna daga babban birnin tarayya da kuma Nyanya da ke Nasarawa.

Kwamishinan walwala da jin dadi ta jihar Kaduna, Hafsat Baba, ta tabbatar da hakan ga gidan talabijin din Channels a ranar Laraba.

Ta kara da cewa an kama almajiran ne a kananan hukumomin Soba da Giwa na jihar.

Jami'in tsaro sun kama matafiya da almajirai 150 a Kaduna

Jami'in tsaro sun kama matafiya da almajirai 150 a Kaduna
Source: UGC

Kamar yadda tace, daga cikin matafiyan 150, 90 duk daga jihar Kano suke yayin da sauran suka fito daga Nasarawa da kuma Birnin Gwari.

Ta kara da bayanin cewa, dukkan matafiyan da almajiran ba 'yan jihad bane kuma an mayar dasu zuwa inda suka fito.

Baba ta jaddada cewa, har a yanzu dokar hana shige da fice a jihar na nan a Kaduna.

Ta kara da jaddada cewa duk wani mutum da zai shigo jihar za a mayar da shi inda ya fito ko kuma a killace shi na kwanaki 14.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jirgin da ya kwaso 'yan Najeriya daga Dubai ya yi juyawar gaggawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kotun tafi-da-gidanka a jihar Kano ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin bulala biyar a kan laifin take dokar takaita zirga-zirga a jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, kotun mai zama a karamar Gwale wacce alkali Salisu Idris ke jagoranta, ta kama mutumin da laifin take dokar tare da yanke masa hukunci.

Amma kuma, wanda ake yankewa hukuncin ya karba hukuncinsa a take.

Kotun ta yankewa mutum 14 hukunci sakamakon kama su da tayi da laifin kaiwa da kawowa ba tare da wani dalili ba.

An yankewa wadanda aka kama hukuncin fansar kansu tare da ayyuka ga yankin da suke a matsayin hanyar hukunta su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel