Coronavirus: 'Ya'yan itatuwa da kayan lambu masu bunkasa garkuwar jiki

Coronavirus: 'Ya'yan itatuwa da kayan lambu masu bunkasa garkuwar jiki

A yayin da likafar annobar korona ke ci gaba babu sassauci, wata kungiyar masu bincike a Jami'ar Fasaha ta Akure da ke jihar Ondo, ta yi wani bincike kan muhimmancin ta'ammali da wasu 'ya'yan itatuwa da kayan lambu masu bunkasa garkuwar jiki.

Sanadiyar yadda kawo yanzu ba a samar da maganin cutar korona ba, a halin yanzu dai ingatacciyar garkuwar jiki ita kadai ce ke iya yakar cutar a jikin mutum kamar yadda mahukuntan lafiya suka bayyana.

Kwararrun masanan na jami'ar FUTA sun bayar da sharawa a kan muhimmancin bunkasa garkuwa jiki ta hanyar ci da kuma shan wasu dangin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu masu tarin sunadarai.

Jagoran masu binciken da ya kasance kwararren masani a fannin kimiya da fasahar abinci, Farfesa Ganiyu Oboh, ya ce kayan lambu da 'ya'yan itatuwa sun kunshi sunadarai masu bunkasa garkuwar jiki.

Farfesa Oboh ya tabbatar da cewa, sunadaran vitamins, minerals, phytochemicals, carotenoids, polyphenol, flavonoids, flavones da flavanones, da ake samu cikin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa, su na yakar cututtuka ta hanyar bunkasa garkuwar jiki.

'Ya'yan itatuwa

'Ya'yan itatuwa
Source: Depositphotos

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar korona, kwararren masanin kayan abinci da sha, ya ce akwai bukatar mutane su yi riko da kayan lambu da kuma kayan itatuwa domin inganta garkuwar jikinsu.

KARANTA KUMA: Asusun Bayar da Lamuni ya danka wa Najeriya tallafin gaggawa na $3.4bn

A halin yanzu dai bincike ya tabbatar da cewa, raunin garkuwa jiki yana da babbar alaka da tsufa yayin da a dukkanin kasashen da cutar korona ta bulla, ta fi kassara dattawa wadanda suka haura shekaru 60 a duniya.

Haka kuma binciken ya nuna cewa cutar korona ta fi illata wadanda suke fama da wasu cututtukan na daban kamar cutar daji, ciwon koda, ciwon suga hawan jini da sauransu.

'Ya'yan itatuwa da kayan lambu wadanda masu binciken suka tabbatar da ribar da suka kunsa ta bunkasa garkuwar jiki sun hadar da; ayaba, karas, mangwaro, tufa, tumatir, abarba, kashu, kankana, lemun zaki, gwanda, goba, da agwaluma.

Masu binciken sun gano wannan 'ya'yan itatuwa sun kunshi sunadaran quercetin, gallic acid, catechin, epicatechin, rutin, da chlorogenic acid wadanda ke da tasirin gaske wajen bunkasa garkuwar jiki.

Sun kuma bada shawarar a yi riko da korayen ganyayyaki da suka kunshi sunadaran antioxidants kamar; vitamins A, vitamins C, vitamins E, beta carotene, da selenium.

Shugaban jami'ar, Joseph Fuluwape, ya ce jami'ar za ta ci gaba da zage dantse wajen tunkarar halin da Najeriya da kuma Duniya ta ke ciki domin fuskantar kalubale ta hanyar bincike da kuma kawo ci gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel