Coronavirus: Najeriya za ta debo 'yan kasarta daga kasashen ketare

Coronavirus: Najeriya za ta debo 'yan kasarta daga kasashen ketare

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara kwaso 'yan Najeriya da suka kasa dawo gida a wasu kasashen ketare sakamakon hana zirga-zirga da annobar korona ta janyo.

Ma'aikatar kasashen wajen Najeriya, ita ta sanar da hakan a kan shafinta na Twitter a ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2020.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce za a killace dukkanin mutanen da za a kwaso yayin shigowarsu Najeriya har na tsawon kwanaki 14 domin a tabbatar ba sa dauke da kwayoyin cutar korona.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta nuna cewa, za a kwaso tawagar farko ta 'yan Najeriya 265 a jirgin saman Emirates daga Dubai a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu.

Ta ce ana sa ran saukar tawagar ta farko da misalin karfe 3.00 na Yammacin ranar Laraba a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Da misalin karfe 7.00 na safiya, za kuma a kwaso wata tawagar 'yan Najeriya 300 daga filin jirgin saman Heathrow da ke birnin Landan a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu.

KARANTA KUMA: Serie A: Ronaldo da iyalansa sun koma kasar Italiya ana tsaka da annobar korona

Za a yi kirdadon saukar tagawar ta biyu a jirgin saman British Airways da misalin karfe 1.30 a wannan rana dai ta Juma'a.

Domin kawar da shakku da daukar matakan tsaro, ma'aikatar tare da hadin gwiwar hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC da kuma sauran hukumomin tsaro, ta kammala duk wani shiri na killace mutanen da za ta kwaso.

Ta kara da cewa, tana ci gaba da shirye-shirye da jirgin saman Ethiopian Airline domin kwaso wata tawagar 'yan Najeriya daga birnin New York na kasar Amurka zuwa Abuja a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Mun ji cewa wata mata cikin tawagar farko ta 'yan Najeriya da aka kwaso a ranar Laraba daga Hadaddiyar Daular Larabawa ta haifi jariri ana tsaka da tafiya a sararin samaniya.

Babbar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri-Erewa, ita ta sanar da hakan cikin sakon kar ta kwana da ta aikewa maname labarai na jaridar The Punch.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel