Covid-19: Abinda ke mayar mana da aiki baya a Kano - Boss Mustapha

Covid-19: Abinda ke mayar mana da aiki baya a Kano - Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce rashin kayan aiki na sanya ido da gano mutanen da aka yi hulda da su ne babbar matsalar da Kano ke fuskanta wurin shawo kan yaduwar muguwar cutar coronavirus a jihar.

Mustapha ya kuma kasance shugaban kwamitin yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa.

Sakataren gwamnatin jihar tare da darakta janar na NCDC da kuma ministan lafiya sun yi bayani ga 'yan majalisar wakilan tarayya a ranar Talata a kan halin da kwamitin ke ciki wajen yaki da annobar a jihar Kano.

Mustapha ya sanar da 'yan majalisar cewa Kano na kokarin zama jihar da ta fi kowacce yawan masu cutar a Arewa.

Covid-19: Abinda ke hana mu mayar mana da aiki baya a Kano - Boss Mustapha
Covid-19: Abinda ke hana mu mayar mana da aiki baya a Kano - Boss Mustapha
Asali: UGC

A halin yanzu, a cikin jama'a ake yada cutar. Ya ce gwamnati za ta samar da cibiyar karbar samfur tare da ma'aikata biyu a kowacce karamar hukumar jihar Kano din.

"Mun tura kungiyar kwararrun ma'aikata 41 daga NCDC don taimakawa jami'ai 17 na hukumar kiwon lafiya ta duniya a jihar.

"Wasu kwararrun a karkashin jagorancin ma'aikatar lafiya ta tarayya suna Kano don samar da taimakon gaggawa tare da karfafa yakar cutar a jihar," yace.

Ya ce PTF na da kayayyakin kiwon lafiya wadanda za ta iya zuwa da su ko ina.

KU KARANTA KUMA: Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona

"Gwamnatin tarayyar za ta samar da karfin kayan aiki don cike gibin da gwamnatin jihar ta bari na yaki da annobar a jihar Kano," yace.

Mustapha ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta samar da dakin kula na musamman da cibiyoyin killacewa a jihohi 36 na fadin kasar nan tare da babban birnin tarayya.

"Kamar yadda na saba fadi, kwayar cutar ta zo ne don janye mana hankali tare da gurbata lafiyarmu da arzikinmu.

"Ana iya ganin illar annobar a bangaren tattalin arziki da kiwon lafiya," cewasa.

Ya yi kira ga majalisar dattijan kasar nan da ta samo sabon salo da zai sa Najeriya ta shirya fuskantar annoba ko a nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel