Yadda Gwamnatin Buhari za ta yi amfani da $311 da aka mayar wa Najeriya cikin kudin da Abacha ya sace

Yadda Gwamnatin Buhari za ta yi amfani da $311 da aka mayar wa Najeriya cikin kudin da Abacha ya sace

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa dangane da yadda za ta yi amfani da dala miliyan 311 da aka mayar wa Najeriya, cikin kudaden da ake zargi tsohon shugaban mulkin mallaka, Janar Sani Abacha ya sace.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta za kashe kudaden ne wajen kammala ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasar.

Ana iya tuna cewa a makon ne dai ministan shari'a kuma lauyan kolu na kasa, Abubakar Malami, ya ce gwamnatin Najeriya ta karbi sama da dala miliyan 311 daga Amurka daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban ya sace.

Malami ya bayyana wannan ne a nanar Litinin, 4 ga watan Mayu a Abuja. Ministan kasar ya yi jawabi ne ta bakin wani Hadiminsa, Dr. Umar Gwandu.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ministan ya fitar, ya ce kudin ruwa ya sa kudaden suka karu daga dala miliyan 308 zuwa dala miliyan 311 daga watan Fabrairu zuwa Afrilun 2020 da aka ajiye su a babban bankin Najeriya.

Dr Gwandu ya ce an dawo wa da Najeriya kudaden ne bayan samun fahimtar juna tsakanin gwamnatin Amurka da gwamnatin Jersey inda ake boye kudaden na marigayi Abacha.

Sai dai babu shakka Amurka da Jersey sun ciri wani kaso na kudin sanadiyar shige-da-ficen shari'a da suka yi na kokarin kwato kudade.

Sanarwar da hadimin ministan ya yi ta nuna cewa gwamnatin Najeriya tun a shekarar 2014 ta fara bibiyar matakan dawo da kudaden da ake yi wa lakabi da "Abacha III."

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu
Source: UGC

Sai dai mun ji cewa, hadimin shugaban kasa Buhari ya ce gwamnatin Amurka da ta Jersey sun yi dakon kwato wa Najeriya kudaden tun a wancan lokaci saboda zargin rashawa da kuma rashin aminci da suka yiwa gwamnatocin kasar nan na baya.

Mallam Garba ya ke cewa Amurka da Jersey sun ki yarda da gwamnatocin Najeriya da suka shude saboda zargin za su sake yin ruf da ciki a kan kudaden.

KARANTA KUMA: Jerin kasashe da cutar korona ta fi yiwa illa a nahiyyar Afirka - WHO

"Wadannan kudaden an riga an kasafta su, kuma za ayi amfani dasu gaba daya, don samar da ababen ci gaba da more rayuwa da aka dade ana dakonsu tsawon shekaru aru-aru."

"Cikin manyan ayyukan da gwamnatinmu za ta kammala sun hadar da; Gadar Neja ta biyu, hanyar Legas zuwa Ibadan da kuma hanyar Abuja-Kaduna-Kano."

"Samar da dubunnan ayyuka ga 'yan Najeriya da horas wa a kan ayyukan gini da kere-kere, wanda kuma za a ci moriyarsu wajen muhimman ayyuka nan gaba."

"Za kuma a yi amfani da wani kaso na kudaden wajen ci gaba da aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla, wanda idan aka kammala, zai samar da hasken lantarki ga kimanin gidaje miliyan uku wato sama da mutum miliyan goma za su amfana a kasar."

A bara gwamnatin Switzerland ta dawo wa Najeriya dala miliyan 320 cikin kudaden da ake zargi marigayi Abacha ya wawure, inda ake ci gaba da amfanarsu wajen tsarin ciyar da daliban makaranta, bayar da tallafin kudi da kuma hatsi ga wadanda suke cikin matsanancin hali.

Mallam Garba ya kara da cewa, da ba don wannan kudaden ba, yaki da annobar korona zai yi wa Najeriya tsananin gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel