CUPP: Bill Gates bai ba mu cin hanci ba – Majalisa ta wanke kanta daga zargi
A zaman ranar talata, ‘yan majalisar wakilan tarayya su ka dauki matakin kai kara kotu a kan zargin da ake yi masu na cewa sun karbi cin hancin kudi domin kawo kudirin rigakafi.
Kungiyar CUPP ta fito ta jefi majalisar wakilai da karbar cin hancin dala miliyan 10 daga hannun Attajirin nan na kasar Amurka, Bill Gates, domin su yi maza su kawo wannan kudiri.
‘Yan majalisar sun musanya wannan zargi, su ka bayyana cewa babu wanda ya ba su wani cin hanci. Ahmed Wase ya fara kawo wannan magana a gaban majalisar a zaman na jiya.
Honarabul Ahmed Wase ya ce bai karbi cin hanci daga hannun kowa ba, kuma bai san wani ‘dan majalisa da aka ba kudi ba. Wannan shi ne ra’ayin Honarabul Alhassan Ado Doguwa.
Femi Gbajabiamila ya ce babu dalilin biyewa irin wadannan karyayyaki. Shugaban majalisar ya ce wannan zargi ya sake nuna akwai bukatar a sa doka kan amfani da kafafen zamani.
KU KARANTA: An samu wadanda su ka kamu da COVID-19 a Zamfara, Kano da Kaduna
Shugaban marasa rinjaye Ndudi Elumelu, ya sa baki a wannan magana, ya ce ya karanta labarin a kafar sadarwa. Elumelu ya ce babu wanda ya biya su kudi domin su amince da kudirin.
Rt. Hon. Gbajabiamila ya ce za su shigar da kara a kotu saboda nauyin zargin da aka jefi majalisar da shi. A cewarsa yin hakan zai zama darasi ga sauran kungiyoyi da ke yin irin wannan.
Obinna Chidoka ya ce mutanensa su na kiransa ya ba su na su kaso na cin hanci da ake zargin ya karba. Henry Nwawuoba shi ne zai jagoranci kwamitin da zai yi bincike a kan zargin.
Shugaban majalisar wakilan ya bukaci akawun majalisar da shugaban masu rinjaye da kuma mai ba majalisa shawara a kan harkar shari’a su fara shirin gabatar da karansu a gaban kotu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng