Coronavirus: Mutanen da annobar ta kama a jahar Kano sun kai 397

Coronavirus: Mutanen da annobar ta kama a jahar Kano sun kai 397

Muguwar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, COVID-19, wanda aka fi sani da suna Coronavirus na cigaba da zamewa al’ummar jahar Kano babbar tarnaki.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Kano ta bayyana cewa zuwa yanzu jimillan masu cutar Coronavirus a jahar sun kai 397 bayan samun sabbin mutane 32 dake dauke da cutar.

KU KARANTA: Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

Ma’aikatar kiwon lafiyan ta bayyana haka ne a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, wanda hakan ya yi daidai da kididdigar hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, kamar yadda ta fitar.

NCDC ta fitar da nata bayanan ne da misalin karfe 11:50 na daren Talata, inda ta bayyana cewa an samu karin mutane 148 da suka kamu da cutar a Najeriya kamar yadda gwaji ya tabbatar.

Coronavirus: Mutanen da annobar ta kama a jahar Kano sun kai 397

Coronavirus: Mutanen da annobar ta kama a jahar Kano sun kai 397 Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

NCDC ta ce jahar Legas ce jahar dake kan gaba wajen yawan masu cutar, yayin da Kano ke matsayi na biyu, Abuja, Borno, Gombe, Katsina da Ogun a matsayin jahohi biyar dake bin Kano.

Sanarwar ta ce an samu mutane; 43 a Legas, 32 a Kano, 14 a Zamfara, 10 a FCT, 9 a Katsina, 7 a Taraba, 6 a Borno, 6 a Ogun, 5 a Oyo, 3 a Edo, 3 a Kaduna, 3 a Bauchi, 2 a Adamawa, 2 a Gombe.

Yayin da jahohin Filato, Sakkwato da Kebbi suke da mutane 1 kowannensu. Da wannan jimillan masu cutar a Najeriya zuwa 2950, mutane 481 sun warke yayin da mutane 98 suka mutu.

A hannu guda kuma jahar Legas tana da mutane 1126 dake dauke da cutar, Kano 397, FCT Abuja 307, Borno 106, Gombe 98, Katsina 92, Ogun 91, Kaduna 84, Bauchi 83 sai Sakkwato ta goma 67.

A wani labarin kuma, kungiyar manyan yan kasuwan Singer ta jahar Kano sun dauki alkawarin rage farashin kayan masarufi domin taimaka ma al’ummar jahar.

Hukumar karbar koke koke da yaki da rashawa, PCACC, ce ta sanar da haka a ranar Talata, inda ta ce yan kasuwan sun dauki wannan alkawari ne bayan wata ganawa da suka yi da ita.

“An cimma yarjejeniya tsakanin PCACC da yan kasuwar Singer kan cewa daga yanzu farashin buhun siga ya koma N16,000, kuma farashin dukkanin kayan abinci zai koma kamar yadda yake a da.

“Amma ban da shinkafa, saboda sun ce a yanzu basu da shi a kasa, don haka hukumar za ta shirya ganawa da kungiyar masu sarrafa shinkafa a jahar don kula da rawar da suke takawa wajen tsawwala farashin shinkafar.” Inji hukumar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel