Hankalin NMA ya tashi bayan Jihar Kogi ta hana yin gwajin cutar COVID-19

Hankalin NMA ya tashi bayan Jihar Kogi ta hana yin gwajin cutar COVID-19

Jaridar Premim Times ta ce kungiyar likitocin Najeriya na reshen jihar Kogi sun nuna damuwarsu a game da kin yi wa mutanen da ake zargin ba su da lafiya gwajin cutar COVID-19.

A ranar Talatar nan, an yi wa mutane kusan 20, 000 gwajin kwayar cutar COVID-19 a fadin Najeriya. jihar Kogi ta na cikin inda har yanzu ba a samu labarin wani mai dauke da cutar ba.

A jihar Kogi, gwamnati ta na hana ayi wa Bayin Allah gwajin cutar COVID-19 da gan-gan. Gwamnatin jihar ta ma fito ta na kukan ana kokarin tabbatar da samun mai cutar a jihar.

Wannan zargi da gwamnatin Kogi ta ke yi na cewa wasu na neman kakaba mata Coronavirus ya jefa likitocin da ke aiki a jihar cikin wani hali, har ta kai kungiyar NMA ta fito ta yi magana.

Shugaban Kungiyar likitocin kasar na reshen jihar watau Dr. Kabir Zubair ya gargadi gwamnatin Yahya Bello game da matakin da ta dauka, ya ce abin da gwamnatin ta ke yi ya na da hadari.

KU KARANTA: Wata akuya ta kamu da cutar Coronavirus a kasar Tanzaniya

A wata hira da Kabir Zubair ya yi da Premium Times, ya nuna tsoronsa a kan kin yi wa mutanen jihar gwajin cutar. Likitan ya bayyana cewa yin hakan zai iya zama matsala ga jihar Kogi.

Ya ce: “Idan har jihar ba ta yi wa kowa gwaji duk da ana samun mutane rututu da ake zargin su na dauke da cutar, hakan na nufin nan gaba za a yi ta fama da masu dauke da wannan cuta.”

Dr. Zubair ya yi gargadi cewa nan da wani lokaci za a rika neman wadanda su ka kamu da cutar a rasa, saboda gwamnati ta ki bari ayi wa mutane gwaji domin a killace masu dauke da cutar.

“Babu yadda za a iya gujewa yaduwar cutar tsakanin al’umma. Kuma wannan wata kwantaciyyar annoba ce mai shirin barkowa da za ta zama mana musiba.” Inji shugaban na kungiyar NMA.

Kwanaki hukumar NCDC ta zargi jihohin Nasarawa, Kuros Riba da Kogi da kin yi wa jama’a sosai gwaji. Chikwe Ihekweazu ya ce jihohin na kokarin boyewa duniya gaskiyar lamarin cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel