An tashi garuruwa guda 7, an kashe jama’a da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba

An tashi garuruwa guda 7, an kashe jama’a da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba

Wani sabon kazamin rikici ya barke tsakanin yan kabilar Tibi da kabilar Ichen a karamar hukumar Donga ta jahar Taraba a ranar Talata, 5 ga watan Mayu.

Daily Trust ta ruwaito an yi asarar dimbin rayuka a yayin rikicin, sa’annan akalla garuruwa 7 ne aka tashe su daga aiki bayan an kona su kurmus, daga ciki har da Anano da Suntai Daji.

KU KARANTA: Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

An ruwaito mayakan kabilun sun mamaye yankin gaba daya, wanda hakan yayi sanadiyyar dubunnan mutane yin gudun hijira domin tsira da ransu, musamman mata da kananan yara.

Wani mazaunin yankin, Dauda Danazumi ya ce mayakan sa kai daga bangarorin biyu ne suka kaddamar da hare hare a kan kauyukan abokan hamayyarsu dauke da muggan makamai.

An tashi garuruwa guda 7, an kashe jama’a da dama a rikicin kabilanci daya barke a Taraba
Rikicin Taraba Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A yanzu haka dubun dubatan jama’an garin sun tsere zuwa Kurmi, Bali, Gassol da kuma Takum don neman tsira, amma yace babu takamaimen adadin mutanen da suka mutu a rikicin.

Shi ma kakaakin rundunar Yansandan jahar, David Misal ya tabbatar da barkewar rikicin, kuma yace bai san iya mutanen da aka kashe ba, amma dai an tura karin jami’ai zuwa yankin.

A kwanakin baya ne aka kulla yarjejeniya tsakanin gwamnatin jahar Benuwe da gwamnatin jahar Taraba na samar da zaman lafiya tare da kawo karshen rikicin kabilun Tibi da Jukunawa.

An kulla yarjejeniyar ne a jahar Nasarawa a karkashin jagorancin mataimakin gwamna Emmanuel Akabe, yayin da mataimakin gwamnan Benuwe da Taraba suka halarci zaman.

Daga cikin matsayin da aka cimma a taron yarjejeniyar sunhada da:

“Akwai bukatar dakatar da duk wasu hare hare daga kowanne bangare domin a samu yan gudun hijira su koma gidajensu, gwamnonin jahohin biyu za su gana da shuwagabannin gargajiyan yankunan da ake rikicin don wayar musu da kai game da bukatar zaman lafiya.

“Za’a yi amfani da kafafen watsa labaru domin cimma burin wayar da kan jama’an, dole ne a kyale yan gudun hijra dake Taraba su koma gidajensu tare da sama musu da tsaro saboda su koma gida su yi noma.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel