A karshe, ministan lafiya ya bayyana magananin da FG ta amince da amfani da shi a kan ma su jinyar covid-19

A karshe, ministan lafiya ya bayyana magananin da FG ta amince da amfani da shi a kan ma su jinyar covid-19

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya ce Najeriya ta fara amfani da wani magani mai suna 'remdesivir' a kan ma su jinyar cutar covid-19.

Da ya ke gabatar da jawabi a gaban mambobin majalisar wakilai ranar Talata, Ehanire ya ce da maganin ake amfani a kan ma su jinyar cutar covid-19 jihar Legas.

Sai dai, ministan bai bayyana irin tasirin maganin a kan cutar covid-19 ba.

"Da remdesivir mu ke amfani; mun fara gwada shi a kan ma su cutar covid-19 a Legas," a cewarsa.

A cewar ministan, an fara amfani da maganin ne domin ganin tasirinsa a kan kwayar cutar covid-19.

Ministan ya ce an kirkiri maganin ne tun asali domin maganin cutar Ebola tare da bayyana cewa Najeriya ba ta da wani zabi da ya wuce ta rungumi amfani da maganin domin maganin cutar covid-19.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu babu wani maganin gargajiya da aka amince da amfani da shi a kan ma su dauke da kwayar cutar covid-19.

A karshe, ministan lafiya ya bayyana magananin da FG ta amince da amfani da shi a kan ma su jinyar covid-19

Ministan lafiya; Osagie Ehanire
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta rawaito cewa ma su jinyar covid-19 sun warke bayan an gudanar da gwajin maganin a kansu.

DUBA WANNAN: Barnar Abacha: Yadda gwamnatin Buhari za ta kashe $311m da Amurka ta dawo da su - Fadar shugaban kasa

Kamfanin da ke kera maganin, Gilead Sciences, ya ce an gano cewa maganin ya na da tasiri a kan cutar covid-19 bayan an fara gwajinsa a kan ma su dauke da kwayar cutar a watan Fabrairu.

Sai dai, kamfanin ya ce har yanzu ba a kammala nazari a kan tsawon lokacin da ya kamata a dauka ana amfani da maganin a kan mai dauke da cutar korona ba.

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasar Amurka (FDA) ta amince da amfani da maganin a kan ma su dauke da kwayar cutar covid-19 da aka kwantar.

Ya zuwa yanzu hukumar lafiya ta duniya (WHO) ba ta amince da amfani da wani magani ko rigakafin cutar covid-19 ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel