Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

Hukumar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da shirinta na yi ma yan wasan gwajin cutar Coronavirus domin tabbatar da matsayin lafiyar yan wasan.

BBC Hausa ta ruwaito hukumar Barcelona ta bayyana haka ne a ranar Talata, inda ta ce za’a yi gwajin ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu gabanin cigaba da gasar La Liga ta bana.

KU KARANTA:Sai bayan bakka ake: Kalli yadda yaron Umar Musa Yar’adua ya tuna da mahaifinsa bayan shekara 10

Matakin na daga cikin sharuddan da aka gindaya ma kungiyoyin kasar Spaniya dake gasar La Liga yayin da ake shirin cigaba da karkare gasar.

Zuwa yanzu an baiwa kungiyoyin Spaniya damar fara gudanar da atisaye yayin da gwamnatin kasar ke shirin janye dokar hana shige da fice a kasar saboda tsoron yaduwar Coronavirus.

Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba
Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba
Asali: Getty Images

Kungiyar Barcelona ta ce hukumar La Liga ta amince mata da ta gudanar da gwajin COVID19 a filin atisayenta saboda amincewa da ta yi da kayan aikin da kungiyar ta tanada.

Ko a yanzu an baiwa yan wasan gasar La Liga daman yin atisaye a daidai da daidai, kafin fara atisayen a rukuni rukuni, haka zalika akwai sauran wasanni 11 kafin karkare gasar ta bana.

Annobar Coronavirus ta kama mutane 219,000 a kasar Spaniya, inda ta kashe mutane 25,613, yayin da mutane 123,000 suka warke.

A wani labarin kuma, wata karamar yarinya yar shekara 6 ta kamu da cutar Coronavirus mai toshe numfashi a garin karamar hukumar Kazaure na jahar Jigawa.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan kiwon lafiya na jahar, kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar Coronavirus a jahar, Abba Zakarine ya bayyana haka a ranar Talata.

Sai Zakarai yace dama mahaifin yarinyar shi aka fara samu da cutar a Kazaure bayan ya dawo daga wata tafiya da yayi zuwa jahar Enugu.

Zakari yace daga cikin mutane 18 da suka yi mu’amala da mahaifin yarinyar, kuma aka musu gwajin cutar Coronavirus, yarinyar ce kawai sakamakon gwajin ya nuna ta kamu da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel