Barnar Abacha: Yadda gwamnatin Buhari za ta kashe $311m da Amurka ta dawo da su - Fadar shugaban kasa

Barnar Abacha: Yadda gwamnatin Buhari za ta kashe $311m da Amurka ta dawo da su - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta fitar da jawabi a kan yadda za ta yi amfani da dalar miliyan $311 da gwamnatin Amurka ta dawowa da Najeriya su ranar Litinin.

Kudin na daga cikin makudan kudaden da tsohon shugaban kasa a mulkin soji, marigayi janar Sani Abacha, ya kwashe daga asusun Najeriya ya boye a bankunan kasashen turai da Amurka.

A cewar jawabin da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, fadar shugaban kasa ta ce za ta yi amfani da kudaden wajen kammala wasu muhimman aiyuka a fadin kasa.

Garba Shehu ya ce gwamnatin kasar Amurka ta ki bawa gwamnatocin baya kudin ne saboda ba ta yarda da su ba, ta na tsoron za su kara sace kudin idan ya shiga hannunsu.

"Tuni an kasafta kudaden, kuma za a yi amfani da su domin kammala wasu muhimman aiyuka da aka yi watsi da su na tsawon shekaru, wadanda su ka hada da: gadar Neja ta biyu, karasa manyan hanyoyin Lagos zuwa Ibadan da Abuja zuwa Kano.

"Za a yi amfani da wani bangare na kudin wajen aikin cibiyar wuta ta Mambilla, wanda idan aka kammala zai samar da wuta ga 'yan Najeriya fiye da miliyan 10 a gidaje fiye da milayan uku.

Barnar Abacha: Yadda gwamnatin Buhari za ta kashe $311m da Amurka ta dawo da su - Fadar shugaban kasa
Garba Shehu da Buhari
Asali: Depositphotos

"Karbar kudin satar a wannan lokaci, da wadanda aka karba a baya daga kasashen Switzerand da UK, babbar dama ce ta sake gina kasa da kudaden da ya kamata a yi amfani da su wajen yin hakan a baya.

"Daga cikin $320m da Najeriya ta karba daga Switzerland ake amfani a shirin ciyar da dalibai da biyan dumbin talakawa tallafin rage mu su wahala.

"Ba don samun wadannan kudaden ba, ba kankanuwar wahala za a sha ba a yaki da annobar covid-19 a Najeriya ba.

"Dawo da kudin ya nuna irin kyakyawar fahimta da girmamawa da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da gwamnatin kasar Amurka," a cewar Garba Shehu.

Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari za ta cigaba da rike kambunta da aka santa da shi a bangaren yaki da cin hanci.

Kazalika, ya bayyana cewa lokacin da 'yan siyasa za su mayar da asusun gwamnati tamkar ATM ya wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng