Yanzu-yanzu: Ban alakanta mace-macen Kano da korona ba - Dr Gwarzo

Yanzu-yanzu: Ban alakanta mace-macen Kano da korona ba - Dr Gwarzo

Shugaban yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa na jihar Kano, Dr Nasiru Sani Gwarzo ya musanta alakanta mace-macen jihar Kano da COVID-19.

Gwarzo ya ce manema labarai ne basu fahimci abinda yake nufi ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Gwarzo ya ce binciken farko na mace-macen jihar Kano da kuma gwaje-gwajen da ake yi na cutar a jihar na alakanta hakan da korona.

Jaridar ta wallafa cewa, "Don haka, kafin kammalar rahoton kwamitin a mako mai zuwa, akwai bukatar jama'ar jihar su tashi daga baccin da suke don daukar matakin gaggawa."

Ya bayyana cewa, a binciken da suka gudanar da kuma tattaunawar da suka yi da 'yan uwan mamata, akwai alamun cutar korona ta taka rawar gani.

Amma kuma, a yayin zantawa da manema labarai a jawabin da ya yi ga kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano a gidan gwamnati, Gwarzo ya ce ba su kammala binciken ba balle su kai ga madafa.

Ya ce babban kuskure ne a wannan lokacin ya bayyana dalilin mace-macen jihar.

Yanzu-yanzu: Ban alakanta mace-macen Kano da korona ba - Dr Gwarzo
Yanzu-yanzu: Ban alakanta mace-macen Kano da korona ba - Dr Gwarzo. Hoto daga Afonjaman
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

Kamar yadda yace: "Wasu daga cikin jaridu sun wallafa cewa cutar korona ce ta ke kashe jama'ar jihar, wannan ba gaskiya bane.

"Har a yanzu jihar na bincike tare da tattaunawa da 'yan uwan mamatan kuma ba a kammala ba.

"Ina son yin amfani da wannan damar wajen musanta abinda manema labarai suka wallafa."

Ya kara da cewa: "Ba alhakin kwamitinmu bane sanar da sakamakon bincikenmu. Gwamnati ce ke da alhakin yin hakan."

Gwarzo ya mika sakon fatan alherinsa ga kwamishinan lafiya na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kwatanta kwazonsa da kokarinsa wajen yaki da cutar a matsayin abin koyi.

Kamar yadda yace, gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar lafiya ta bada tallafin motocin daukar marasa lafiya hudu, na'urorin taimakon numfashi da kuma kayan kariya 200 ga gwamnatin jihar Kano.

Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan taimakon gaggawa da ya kaiwa jihar ta hanyar amsa kiran masu ruwa da tsaki na Kano. An ba jihar tallafi na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel