An shiga zullumi bayan alamomin cutar COVID-19 ta kashe wasu mutum 4 a wata jihar arewa

An shiga zullumi bayan alamomin cutar COVID-19 ta kashe wasu mutum 4 a wata jihar arewa

An shiga tashin hankali a Lokoja, babbar birnin jihar Kogi bayan labarin mutuwar wasu marasa lafiya hudu wadanda suka nuna alamun cutar COVID-19 a cibiyar lafiya ta tarayya ya bazu.

Wani rubutu da aka wallafa a shafin Twitter wanda ya yi fice a shafin na soshiyal midiya a ranar Litinin ne ya rura wutar rade-radin.

“A ranar Asabar, wani mara lafiya ya mutu a FMC, Lokoja, jihar Kogi, bayan ya nuna alamun cutar korona. An dauki samfurinsa.

"Wannan shine mutum na hudu da ya mutu a FMC cikin makon da ya gabata kadai. Ko sau daya ba a dauki samfurin marasa lafiyan ba, imma a raye ko a mace. Duk rufa-rufa ne.

An shiga zullumi bayan alamomin cutar COVID-19 ta kashe wasu mutum 4 a wata jihar arewa

An shiga zullumi bayan alamomin cutar COVID-19 ta kashe wasu mutum 4 a wata jihar arewa
Source: UGC

“A ranar 22 ga watan Maris ne wannan al’amari na farko ya faru. Wata mara lafiya wacce ta shigo Kogi daga Lagas ta bukaci tiyata. Mara lafiyar ta nuna alamun COVID-19, wanda hakan ya sa asibitin suka nemi yi mata gwaji. Ba a amince ba.

"An killace mara lafiyar na dan wani lokaci, an yi mata tiyata sannan aka sallame ta ba tare da an yi mata gwaji ba.

“A makon da ya gabata, akwai wasu marasa lafiya a bangare O&G wadanda suka bayyana matsaloli na numfashi, sun gaza yin numfashi, da sauran alamu na korona.

"Uku daga cikinsu sun mutu. Sun zo ne daga asibitin kudi, daya a Lokoja, daya a Okene, sannan na ukun a Ogudu.

“Ta farkon, Misis GI, mai shekaru 43, wacce ta isa asibitin a ranar Alhamis, ta kasance da zafin jiki da ya kai 38.8°C. Sauran biyun sun kasance da zafin jiki sama da 40°C. Cikin dukkaninsu, babu wanda aka dauki samfurinsa kafin ko bayan mutuwarsu ba.

“Yanzu, a ranar karshe na makon, an kwantar da wani mara lafiya a bangaren hatsari da gaggawa (A&E) da zafin jikin da ya kai 40.3°C sannan aka mayar da shi bangaren maza. Mara lafiyan ya shafe sa’o’i uku a bangaren sannan ya mutu.

“Wani mara lafiyan kuma ya bayyana alamun COVID-19 a ranar Lahadi amma duk wani yunkuri na daukar samfurinsa bai cimma nasara ba; a jiya, mara lafiyan ya mutu” wani Fisayo Soyombo, ya yi zargi a shafin twitter na @fisayosoyombo.

Ya ce an gargadi FMC din cewa idan suka take tsarinsu na aika samfurin wani zuwa NCDC, za a rufe su cibiyar kan hujjar tarayya da mai cutar.

Ya kuma bayyana cewa babu ko daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar da ke asibitin SDG/FAREC, Kogi State Diagnostics Centre da kuma asibitin Maimuna and Usman Yahaya Foundation da ya kammalu domin fara aiki a ciki.

“Ba za a iya kai mara lafiya ko daya daga cikinsu ba. Waje guda daya kammalu shine a asibitin kwararru na jihar Kogi, Lokoja, inda aka taba kula da masu cutar Lassa. Kuma yana dauke da gadaje hudu ne kawai.

"Dukkaninsu gini ne kawai, babu kayayyaki ko daya don amfanin likitoci.”

Lamarin na zuwa ne a lokacin da kungiya ma’aikatan lafiya na hadin gwiwa (JOHESU) ke tsaka da barazanar janye ayyukansu kan yanayi wanda ke jefa mambobinsu cikin hatsari, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban JOHESU, Kwamrad Obajemu Samuel, ya bayyana cewa a kullun ma’aikatan lafiya a FMC suna cikin hatsari na kamuwa da cutar tunda ba a samar da kafar yi wa marasa lafiya gwaji domin sanin matsayinsu ba.

Ya bayyana cewa ma’aikatan sune marasa gata saboda rashin sama masu kayan

kare kai domin tsare kansu daga kamuwa da cutar.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa

Hakazalika, kungiyar likitocin Najeriya ta hannun shugabanta, Dr Zubairu Kabir ta koka kan rashin fagen yi wa marasa lafiya da suka nuna alamun coronavirus gwaji, ta yi gargadin cewa lamarin ka iya yada cutar.

Ba a samu damar jin tabakin babban daraktan lafiya na cibiyar, Dr Olatunde Alabi ba, domin baya daga waya kuma bai amsa sakon waya da aka tura masa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel