COVID-19: Korona ta halaka likita daya, 30 sun kamu a Kano

COVID-19: Korona ta halaka likita daya, 30 sun kamu a Kano

Sama da likitoci 30 ne a asibitocin kudi da na gwamnati a jihar Kano suka kamu da cutar korona, kamar yadda kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta bayyana.

Shugaban NMA na reshen jihar Kano, Dr Sanusi Mohammed Bala ya tabbatar da cewa daya daga cikin likitocin da suka kamu da cutar a jihar ya riga mu gidan gaskiya.

Ya bayyana cewa, da yawa daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun sameta ne ta hanyar duba marasa lafiya wadanda suka zo asibitin ba tare da sun san suna dauke da cutar ba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, goma daga cikin likitocin da suka harbu da cutar duk ma'aikata ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Shugaban likitoci masu neman kwarewa na asibiti Malam Aminu Kano, Dr Abubakar Nagoma Usman ya dora laifin halin da suke ciki da rashin kayan kariya.

Ya ce gangancin marasa lafiyan ta yadda suke boye bayanai ga likitocin ya taka rawar gani wurin yada muguwar cutar.

COVID-19: Korona ta halaka likita daya, 30 sun kamu a Kano
COVID-19: Korona ta halaka likita daya, 30 sun kamu a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Rashin abinci da magani yasa masu korona sun fito zanga-zanga a Gombe (Hotuna)

"Wannan cutar na kamanceceniya da zazzabin Lassa saboda wasu marasa lafiyan na nuna alamun cutar. Suna zuwa da alamun cutar amma idan ka fara duba su ko fara basu magani, sai ka gano suna dauke da cutar.

"Daga nan kuwa lokaci ya kure balle mutum ya kare kansa. A saboda haka ne muke kira ga kowa da ya fifita kayan kariya a kan komai gudun yaduwar cutar ga masu taimako," yace.

A yayin zantawa a kan halin da likitocin ke ciki, Nagoma ya ce wasu daga cikinsu suna samun sauki yayin da wasu ke ci gaba da nuna alamun ciwon. Ya ce wasu daga cikinsu na cibiyar killacewa.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa baya ga likitocin, a kalla shida daga cikin 'yan kwamitin yaki da cutar ta jihar sun kamu da kwayar cutar. Suna cibiyar killacewa ta jihar inda suke karbar magani.

Idan za mu tuna, Dakta Bala da Dakta Nagoma sun bayyana damuwarsu a kan rashin kayayyakin kariya da likitocin ke fuska a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel